Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Alƙalin Jihar Ribas, Mai Shari’a Simeon C. Amadi, ya ƙi amincewa da buƙatar majalisar dokokin jihar na kafa kwamitin bincike mai mambobi bakwai domin binciken zargin aikata manyan laifuka da ake yi wa gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma-Odu.
Babban alƙalin ya bayyana cewa akwai umarnin kotu da har yanzu ke aiki, tare da ƙarar da ke gaban kotu ta ɗaukaka ƙara.
Matsayar mai shari’a Amadi na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa ta hukuma da ya aikawa kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, inda ya tabbatar da karɓar buƙatu guda biyu daga Majalisar da ke ɗauke da kwanan watan 16 ga Janairu, 2026.
An miƙa buƙatun ne bisa tanade-tanaden Sashe na 188(4) da 188(5) na ƙundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima bayan Majalisar ta yanke shawarar fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa daga muƙami.
Sai dai a cikin wasikar, Babban alƙalin ya ce, “Dole ne ɓangarorin da abin ya shafa da kuma kotu su jira sakamakon ƙarar da ke gaban kotun ɗaukaka ƙara.”
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka hannuna a ɗaure yake, kasancewar akwai umarnin wucin-gadi na kotu da kuma ɗaukaka ƙara kan waɗannan umarni. Don haka a wannan lokaci, doka ba ta bani damar aiwatar da aikina a ƙarƙashin Sashe na 188(5) na Kundin Tsarin Mulki ba.”
