
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro a shiyyar Arewa ta Gabas da ke aiki a ƙarƙashin tawagar Atisayen Haɗin Kai (OPHK), sun yi wata gagarumar nasara a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan tallafa wa ta’addanci a yankin.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na jami’an haɗaka na OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar a yau Lahadi, jami’an sun yi nasarar kama wata tsohuwa mai suna Hauwa Abdlazeez ‘yar kimamin shekara 65 a ranar 23 ga watan Junairu, 2026.
An kama matar, wadda ake zargin ta da yi wa ‘yan ta’adda dillancin miyagun ƙwayoyi ne a Ƙaramar Hukumar Askira Uba da ke Jihar Borno bayan samun wani bayanin sirri.
Kanal Uba ya bayyana cewa ana zargin tsohuwar tana daga cikin masu yi wa mayaƙan Boko Haram safarar tabar wiwi, waɗanda ke gudanar da ayyukansu a yankunan Askira Uba, Rumirgo, Gwahi, Wamdiyo, Uvu da kuma Gaya.
Ya ce, an gano cewa wadda ake zargin tana dakon miyagun ƙwayoyin ne tun daga Ƙaramar Hukumar Sarti Baruwa a Jihar Taraba, sannan ta bi ta wasu hanyoyi da dabaru wajen isar wa mayaƙan.
Kazalika, jami’in ya ce a yanzu matar tana hannu kuma ana gudanar da bincike akanta yayin da ake ƙoƙarin daƙile dukkan hanyoyin da ake bi wajen yi wa ‘yan ta’addar safarar ƙwayoyi.
A ƙarshe, ya ce dakarun suna aiki tuƙuru wajen ganin sun daƙile nau’ukan ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
