Yadda za a kasafta biliyoyin Naira a yarjejeniyar gwamnati da ASUU

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Manyan jami’o’in Gwamnatin Tarayyar Nijeriya sun samu gagarumar ƙaruwar kuɗi bayan amincewar Gwamnatin Tarayya da ƙarin albashi kashi 40 ga malaman jami’a tare da ɓullo da sabbin alawus-alawus masu tsoka.

Binciken kasafin kuɗi na shekarar 2026 da jaridar News Point Nigeria ta gudanar ya nuna cewa rabon kuɗin ma’aikata ga manyan jami’o’i 20 na Gwamnatin Tarayya ya tashi daga naira biliyan 438.85 a 2025 zuwa naira biliyan 533.1 a 2026, wanda ke nuni da ƙarin naira biliyan 94.25, wato kusan kashi 22 cikin ɗari a shekara guda.

Wannan ƙaruwar kuɗi ya biyo bayan wata babbar yarjejeniya da aka cimma a ranar Laraba tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar Malaman Jami’a ta ASUU, wadda ta kawo ƙarshen tsawon shekaru 16 na taƙaddama kan sabunta yarjejeniyar 2009.

Masana na ganin wannan mataki zai taimaka wajen inganta walwalar ma’aikata, tabbatar da daidaiton kuɗi a fannin ilimi da kuma samar da zaman lafiya a harkar aiki a jami’o’in gwamnati, wanda a baya ya sha fama da yawan yajin aiki sakamakon rashin cika alƙawurra.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin albashi kashi 40 ga dukkan malaman jami’o’i tare da samar da wani sabon alawus na musamman da aka kira “Professorial Cadre Allowance” wanda zai bai wa farfesoshi ƙarin sama da naira 140,000 a kowane wata.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya tabbatar da cewa an riga an tanadi kuɗaɗen da za a biya wannan sabon tsarin albashi da alawus. Yayin da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television, ya ce gwamnatin ta tanadi kuɗaɗen da za su tallafa wa ƙarin albashi da kuma sabbin alawus-alawus tara da aka tsara.

A cewarsa, “Farfesa zai riƙa karɓar ƙarin sama da naira 140,000 a kowane wata, sakamakon amincewar Shugaba Bola Tinubu da sabon nau’in alawus ga malaman jami’a. Yanzu muna da kuɗin da za su rufe ƙarin albashi kashi 40 da aka amince da shi, tare da alawus-alawus tara da aka tsara.”

A kasafin kuɗin 2026, Gwamnatin Tarayya ta ware naira tiriliyan 3.52 ga bangaren ilimi, wanda ke wakiltar kashi 6.1 cikin ɗari na jimillar kasafin ƙasa na naira tiriliyan 58.18. Daga cikin wannan, an ware naira biliyan 113.764 ga shirye-shiryen tallafin ilimi, naira biliyan 42 ga shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, da kuma naira biliyan 35 don magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

Sauran kuɗaɗen sun haɗa da naira biliyan 28 domin tsaro a kwalejojin haɗin gwiwa 118 na gwamnati, da kuma naira biliyan 5.2 domin kula da ɗaliban Nijeriya 1,532 da ke karatu a ƙasashen waje.

Bincike ya nuna cewa jami’o’i da dama sun samu ƙarin kuɗin ma’aikata, ciki har da Jami’ar Ibadan, Jami’ar Legas, Jami’ar Najeriya Nsukka, Jami’ar Ahmadu Bello, Jami’ar Obafemi Awolowo, Jami’ar Benin, Jami’ar Jos, Jami’ar Calabar, Jami’ar Ilorin da Jami’ar Abuja.

Jami’ar Ibadan ce ta fi samun ƙarin kuɗi, inda rabon kuɗinta ya tashi daga naira biliyan 25.13 zuwa naira biliyan 37.52. Haka nan Jami’ar Ahmadu Bello ta samu karin sama da naira biliyan 10.5. Sauran jami’o’i ma sun samu ƙarin kuɗi mai yawa.

Sabon tsarin albashi na sa ran zai rage yawan rikici tsakanin gwamnati da malaman jami’a tare da taimakawa wajen daƙile yajin aiki da ya daɗe yana tarnaƙi ga tsarin karatu a Nijeriya.

By ukarofi