Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dakta Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana cewa rashin haɗin kai da ƙarancin fahimtar al’amuran zamani na daga cikin manyan dalilan da ke hana malamai taka rawar gani wajen ci gaban al’umma.
Dakta Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani taron nazari da Jami’ar Bayero Kano ta shirya domin tunawa da rayuwa da koyarwar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Ya ce malamai na da rawar da za su taka wajen gyaran al’umma idan har suka haɗa kai suka rungumi ilimin zamani tare da na addini.
Malamin ya jaddada cewa rarrabuwar kai a tsakanin malamai na haifar da rikice-rikice da rashin fahimta a cikin al’umma.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ba da muhimmanci ga makarantun allo ta hanyar samar da tsari mai dorewa da zai hana bara da talauci a tsakanin almajirai.
Masu ruwa da tsaki a taron sun yaba da jawaban Dakta Gumi, suna masu cewa hakan ya dace da halin da ƙasa ke ciki.
A ƙarshe, an yi kira ga malamai da su zama abin koyi wajen haƙuri, fahimtar juna da haɗin kai domin samar da al’umma mai zaman lafiya.
