Nijeriya ta dawo sahun gaba a taron tattalin arzikin duniya – Shettima

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya dawo Abuja bayan kammala wata ziyara ta mako guda zuwa Guinea-Conakry da kuma Switzerland, inda ya bayyana cewa Nijeriya ta sake komawa sahun gaba a tattaunawar tattalin arziki da manufofin duniya.

A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, ya fitar, an ce Mataimakin Shugaban ƙasar ya iso Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Asabar.

Shettima ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, kafin daga bisani ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron shekara-shekara na 56 na World Economic Forum (WEF) da aka gudanar a Davos, Switzerland.

A cewar Shettima, ziyarar ta nuna sabuwar jajircewar Nijeriya wajen ƙarfafa haɗin kai a yankin Afirka ta Yamma da kuma ƙoƙarin sake fasalta tattalin arzikin ƙasar ƙarƙƙshin ajandar “Renewed Hope” ta gwamnatin Tinubu.

A Conakry, Mataimakin Shugaban ƙasar ya jaddada rawar da Nijeriya ke takawa a ƙungiyar ECOWAS, tare da buɗe ƙofar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu musamman a ɓangaren noma da masana’antu.

Daga nan ne ya wuce Davos domin halartar taron WEF 2026, inda ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ɗauki hankali shi ne ƙaddamar da “Nigeria House Davos” – rumfar zuba jari ta farko da Nijeriya ta kafa a wajen taron. An bayyana rumfar a matsayin cibiyar dindindin da ke nuna damar zuba jari a ɓangarorin ma’adanai, noma da tattalin arzikin zamani na dijital.

Yayin da yake jawabi a wani zama na musamman mai taken “When Food Becomes Security,” Shettima ya bayyana sabon tsarin tsaron abinci na ƙasa, inda ya ce noma ya zama ginshiƙi na tsaron ƙasa da kwanciyar tattalin arziki.

Haka kuma, ya halarci tattaunawa tare da tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Yemi Osinbajo da Ministan Kuɗi Wale Edun, a ƙarƙashin shirin “Accra Reset Initiative,” wanda ke ingiza masana’antu a Afirka ta hanyar amfani da jarin cikin gida maimakon dogaro da tallafin ƙasashen waje.

Game da tattalin arziki, Shettima ya shaida wa masu zuba jari cewa alamomin tattalin arzikin Nijeriya na ƙara daidaita, inda ya ambaci hasashen bunƙasar GDP da kashi 4.4 cikin ɗari a shekarar 2026 da kuma saukar hauhawar farashi zuwa kashi 12.94 cikin ɗari.

Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na shirin zama ƙasa mai fitar da man fetur da aka tace zuwa ƙasashen waje, musamman da dogaro da matatar Dangote, tare da ƙaruwar fitar da ƙwararrun matasa masu ƙwarewar fasahar dijital zuwa kasuwannin duniya.

By ukarofi