Shin amsa sunan Larabawa watsi da al’adar Bahaushe ne?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Wani shafin yanar gizo mai taken THE NIGERIAN BAHAUSHE ya yi wuf ya wallafa wani rubutu da ɗaya daga ‘yan Hausa zalla Aliyu Ammani ya rubuta tun 2019 ya na nuna fargaba cewa sunayen gargajiya na Hausawa za su bace don daukar na Larabawa. Ammani bai tsaya ba sai da ya caccaki wani abu da ya zayyana da wankewa Hausawa kwakwalwa da nau’in musulunci na daban da Jihadin Sakkwato (na Shehu Mujaddadi) ya kawo na goge duk wasu alamu da al’adu na Hausawa kafin zuwan Musulunci. Ammani dai a nan bai kawo aya ko Hadisi daga Alkur’ani ko BIBLE da ke nuna wani nau’in Musulunci ko addini ne da ke da ƙa’idar adana alamu da al’adu na Hausawa kafin zuwan Musulunci ko Kiristanci ba. Shin idan Musulmi su ka ɗauki sunayen Larabawa, Kirista su ka ɗau na Turawa me bambancin a nan. Duk rubutun na sa bai soki Turawa da su ka shigo bayan Jihadin ba a 1903 da a ka yi ruwan sunaye irin su John, Jacob, Peter, Daniel Musa, Paul Audu da sauransu.

Ammani ya kara da cewa idan Bahaushe ya radawa ɗansa suna Faisal ko Fahad wato tsoffin sunayen sarakunan Saudiyya ba malami (musulmi) da zai yi magana. Sai ya ce amma in an juya sunayen kai tsaye zuwa Hausa wato TAKOBI ko DAMISA za a yi mamakin irin kururuwar da za a yi. Mutumin nan bai tsaya nan ba sai da ya dira kan ƙabilancinsa da nuna Fulani na raɗawa ‘ya’yansu Bello, Tukur, Sambo kuma ba wanda ya ke duba sahihancinsu a Musulunci. A nan ya nuna ai duk sunayen Muhammadai ne wato misali Muhammadu Bello ko Muhammad Tukur da wato ba malamin da ke ƙorafi, sai caraf ya ƙara dira kan manufarsa ya na mai cewa amma in an ambata Muhammadu Jan-Gwarzo, Muhammadu Jan Hazo, Muhammadu Korau da sauransu sai a dauka ko soke su da sabawa musulunci. Tambaya a nan shin waye ya dauki waɗannan sunaye sun sabawa Musulunci? A ina? A ABU, BUK, UDUS ko FUDMA ta su Daniel Danladi Musa?

Nan masu muhawara su ka shiga nuna ai su in sun haifi ‘ya’ya sunayen Hausawa za su saka wato don su ba wa Shehu Mujaddadi haushi. Shin Mujaddadi Balarabe ne ko shi ne addinin musulunci? Shin tun kafin Jihadin Shehu ba a yi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ba? Ba a yi mai sunan Larabawa Muhammadu Al-Walid ba? Su ma Jihadin ne ya ƙaƙaba mu su sunayen ko akwai makiya Musulunci a tsakanin wancan zamani gabanin Jihadi da su ka bunne Musulunci su ka ɗauki tsafe-tsafe da camfe-camfe da rawar banjo?.

Shi kansa marubucin Aliyu Ammani tun 2019 zuwa yau bai sauya sunansa ALIYU na Larabawa ba. Shin ko Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ne ya tilasta shi ya cigaba da amfani da sunan? Mutanen nan su na yin abun da su ka ga dama kuma akwai manufar da su ke ɓoyewa. Akwai wani matashi ma mai sunan Sahabban Manzon Allah Abubakar da Usman (Aboubacar Cerdic Ousmane) da ya nuna mahaifinsa ba zai hana shi sauya sunansa ba in ya na so, kuma shi in ya haifi yara sunayen gargajiya na Hausawa zai saka da ke nuna ya na matuƙar tsanar sunayen sahabban Manzon Allah. Da ya ke mutanen ma ƙirƙirar sunayen su ka yi ba sunan gaskiya, ba hoto ba adireshi don haka ko yanzu za su iya ƙaƙalo wani sunan don ɓatar da sawu. Wani abun takaici ma na rashin sanin ya kamata, sai ma ‘yan iƙirarin Hausa zalla na ƙirƙirar sunayen musulunci da na Larabawa kamar AL-HAWSAWI, AL-FARISI, ALKANAWY da sauransu, su na makalawa kansu. Haƙiƙa duk su na yin hakan ne don dabarun bagaye ko basaja don a dauke su masu bin Musulunci sau da kafa don samun logar yaudarar al’ummarmu a bi kiran da su ke yi na aukawa gubar ƙabilanci.

Wallahi na samu sahihin labarin wasu daga masu ruruta fitinar nan jikokin jami’an soji ne da Turawa su ka yi amfani da su wajen rusa Daular Musulunci ta Sokoto don haka sun gado ƙiyayyar ce.

Gari ya waye duk an gane wakilan su Chukwuma da Kanu, kuma ba za su yi nasara ba. Yo ba akwai ma wani a cikinsu da sunansa kakaf takwaran mahaifin Manzon Allah ba ne? su shiga sauya sunayensu ma na zuwa gargajiya ai tsarin mulkin Nijeriya bai hana su raɗawa kansu sunaye har irin su Bob Marley ko Zidane Kajuru ba.

Wallahi ba ma jin haushin kowa ya yi addininsa don hatta tsarin mulkin Nijeriya ya ba wa duk ɗan ƙasa hurumin yin addinin da ya kwanta ma sa a rai ko ma mutum ya zauna ba addinin. Babban laifin shi ne shigar burtu da alamun wani addini don cimma wata manufa mai muni. Idan mutum ya shiga rintsi na barazana ga rayuwarsa kamar abun da ke faruwa a baya a Gonin Gora ko ma a Filato zai iya fakewa da wani addini in ya ga hakan zai kuɓutar da rayuwarsa. A kamfen din ruruta fitinar ƙabilanci a Arewa kusan kakaf masu kamfen ɗin na buya da alamun Musulunci don yaudarar al’ummarmu su saurari sharrin da su ke yayatawa. Yo tun da a kowace ƙabila akwai mabiya addinai daban-daban, me ya sa masu wannan farafaganda ba za su yi amfani da addininsu ba?. Rankatakaf muradin kamfen ɗin yaƙi da tarbiyyar addini ne ba ’yan ta’addan daji ba.

Ni dai tabbas duk ranar da mutanen nan su ka fito a mutane don bayyana ra’ayinsu ko da na yaƙi ne ba zan sake kula su ba don wannan ba aiki na ba ne. Yanzu dai ba zai yiwu na ga wasu mutane na barazana ga zaman lafiya da amfani da sunayen karya AL-waye-waye Abu waye irin samfurin ’yan ta’adda ba, na kau da kai su cigaba da dabdalarsu. Ba zai yiwu wani ya sa alamun mai bin addini ya na ɗabi’ar bangaranci ta ƙabilanci da shaidanci na kyale shi ba. Ba zai yiwu wani da ba shi da alaƙa da Hausa ko Hausawa ba, hasalima ma ya na magana ko rubutu da garma-garmar Hausa ya bugi kirji wai shi ne shugaban ƙungiyar Hausawa na zura ma sa ido ba. Ni na san darajar harshen Hausa kuma tun ina firamare ban taba faduwa jarrabawa ko kaucewa darasin Hausa ba. Duk wadanda mu ka yi karatu da su har zuwa kolejin horon malamai sun san yadda na ke karatu ko rubutun Hausa. Farfesa Tahir Inuwa na jami’ar jihar Gombe zai iya zama shaida. Allah ya sakawa malamanmu da alheri ya jiƙan waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya.

Duk zaluncin mutum ya san addinin Musulunci ya yi tasiri wajen bunƙasa harshen Hausa kuma Hausa harshen addinin musulunci ne. Duk tsaurin ra’ayin mutum in ya na magana ko rubutu da Hausa sai ya yi amfani da kalmomin musulunci, amma hakan ba dalili ba ne na shigar burtu da alamun Musulunci wajen cimma burin kwangilar kunnawa Arewa wuta don kafa ƙasar Biyafara da yankin ƙirƙira na Bel.

Wata babbar alama ta tabbatar da ba ruhin addini a jikin ‘yan bazata masu karyar Hausa zalla ita ce ta nuna wai a dole a ka saka su, su ka auka ƙabilanci. Ka ji rashin gaskiya. Mutanen nan dama fa tsundum a kabilancin su ke don ba Hausawa ba ne, hasalima bambancin ƙabila da addini ya sa dakarunsu ke tare Hausawa da sauran waɗanda su ka tsana a hanya su kashe da tarwatsa kan gawa da manyan duwatsu ruwan kwakwalwa ya kwarara a kan titi. Na ga wani ma da ya nemi lashe jini a jikin wuƙar da ya yi gunduwa-gunduwa da naman wanda ya kashe. Wallahi akwai faifan bidiyon da na gani su na daga-daga dugu-dugu da naman mutanen da su ka tare su a hanya su ka kashe. Ba kuskure ba ne a ayyana su da zama Danjuma da Danjummai da ‘yan ta’addan daji kuma da yardar Allah duk ƙarshensu ya zo.

KAMMALAWA

Yo tun da ba Hausawa ba ne, sun ki jinin a kawo mu su batun addini, don haka sai su ka sauya loga daga kamfen ɗin an tilasta mu su yin ƙabilanci zuwa wai kishin ƙabila su ke yi, oh ƙarfin hali barawo da sallama. In ka ga mutum ya na rubuta I AM PROUDLY kaza da kaza to ya ɗauki ɗabi’ar gingima-gingiman Maguzawa ‘yan caburos masu bautar GIJI da gizagizai. Kar kowane mai addini ya kuskura ya mutu ya na ƙabilanci ko fakewa da kishin ƙabila ya na ƙabilanci. Lallai Musulmi ya tsaya a kan kishin addininsa. Wani ɗan ba ruwanmu ma sai ka ga ya na tuhumar mai ya sa za mu damu don kawai Hausawa sun ce za su kafa ƙungiya; ka ji shirme yaushe su ka zama Hausawa kuma wa ya isa ya hana wani kafa ƙungiya matukar ba ta zunduma ashar da yi wa malamai sharri ba ne.

‘Yan Biyafara sun maida ’yan bazata makamashin kunna fitina a Arewa don samun damar kafa Biyafara a bulus. Miyagun kan yi ta surutu wai Hausawa daban Fulani daban, sai ka ga wani bagidajen Ibo ya na cewa ai na dauka daya ne me bambancinsu?. Haƙiƙa babu Bahaushe da ya sha ni’imar addini da ke cikin wannan tafiyar su Ciwake da Kefas ko kokarin ganar da Igbo wai waye kaza ko waye ba kaza ba. Duk wanda ka ga ya raina kansa ya zama dan barandar IPOB ai sai dai daga yankin Bel da miyagun iri ke ta kururuwar kafawa amma hakan ya gagara don ai gini ba ya zama kan tubalin toka.

By ukarofi