
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yunƙuri na neman kotu ta sake masa kadarorinsa da ta riƙe na wucin-gadi, Tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa ya samu miliyoyin kuɗaɗe daga albashi da alawus-alawus da kuma kyautaka a matsayinsa na jami’in gwamnati.
Malami ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sabon ƙorafi akan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), wadda da fari ta samun izinin kotu na ƙwace kadarori guda 57 da aka alaƙanta su da Malami da ‘ya’yansa biyu.
Ya bayyana cewa N374.6m daga albashi da alawus-alawus, sannan N958m a matsayin kyaututtuka daga abokai na kusa. Haka kuma, akwai Naira biliyan 10.17 daga kasuwanci masu zaman kansu, kamar yadda wasu rahotanni suka shaida.
Malami ya faɗi haka ne ta hannun lauyansa, Joseph Daudu, SAN, a takardar buƙatar da ya shigar a gaban kotu domin neman ta soke umarnin wucin-gadi ta ba wa EFCC na ƙwace kadarorin.
Lauyan ya ce, tuni Malami ya bayyana hanyoyin samun dukiyarsa a takardar bayyana kadarori da ya miƙa wa Hukumar Binciken Ɗabi’a (CCB), inda ya lissafa cewa:
“Ya samu N374,630,900 daga albashi, alawus, estacode, da sauran kudade na aikin gwamnati. Ya samu N574,073,000 daga sayar da wasu kadarori da ya mallaka. Ya samu N10,017,382,684 a matsayin kudin shigar kasuwanci (turnover). N2,522,000,000 kuɗaɗe ne da aka ba kasuwancinsa a matsayin bashi. N958,000,000 kyaututtuka ne na gargajiya daga abokai da ‘yan uwa. N509,880,000 kudade ne da ya samu daga kaddamar da littafinsa mai taken “Contemporary Issues on Nigerian Law and Practice: Thorny Terrains in Traversing the Nigerian Justice Sector – My Travails and Triumphs’,” kamar yadda jaridar QA TV ta ruwaito.
Malami ya kuma buƙaci kotun da ta ɗage kwace aƙalla gidaje uku daga cikin 57 da EFCC ta keɓe domin yiwuwar ƙwace su ga Gwamnatin Tarayya, yana mai cewa kadarorin sun samo asali ne daga halaltattun hanyoyin da ya bi wajen mallakar su.
A ɗaya bangaren kuwa, EFCC ta dage cewa tana da ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa wasu daga cikin kadarorin an same su ne daga haramtattun kuɗaɗ, saboda haka wajibi ne a bar kotu ta yi cikakken bincike kafin yanke hukunci a kai.
