Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara tayi watsi da jita Jihar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewar ta tsaida ɗan takarar ta a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar ne Yusuf Idris ya bayyana hakan ga manema labarai yau Talata.
A cewar sa jita jitar ƙarya ce tsagwaron ta, yana mai bayyana cewar masu yaɗa jita jitar sunyi ne bada yawun jam’iyyar ba.
“Ina amfani da wannan damar in sanar da cewar har yanzu jam’iyyar APC a jihar Zamfara babu wani ɗan takara da aka zaɓa. Ya ce
“Haka zalika zancen da ake yi na cewa mun tsaida ɗan takara ba shi da asali, kuma ba daga jam’iyyar APC ya fito ba a hukumance”.
Yusuf Idris ya kuma buƙaci magoya bayan jam’iyyar ta APC a Jihar da su ci gaba da kwantar da hankalin su tare da ci gaba da aikin gina jam’iyyar.
“Muna maraba da kowane ɗan takara da ya shirya ƙetare kujerar takara a jam’iyyar APC, amma a bar lokaci ya yi.”
A cewar sa duk wani ɗan takarar da zai fito a jam’iyyar ya kamata a zaɓe shi ta hanyar zaɓen fidda gwani na jam’iyyar”.
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa za a yi amfani da tsarin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar wajen zaɓen ɗan takara a shekarar 2027.
