Lamiyya: Nazarin waƙar  ‘La’ila’ ta Alhaji Auwal Umar Dangawuna

Spread the love

Daga MD ASNANIC

1.0 Gabatarwa

Bayyanannen abu ne cewa, mutanen da suka fara tsara waƙoƙi musamman domin yabon Annabi Muhammad (SAW) a duniya sun haɗa da: mahaifiyarsa Aminatu ‘yar Wahabi da kakansa Abdulmuɗallib ɗan Hashim da mai rainonsa Halimatus Sa’adiya. Sai dai mutanen da suka fi shura a yabonsa bayan risala sun haɗa da Hassanu ɗan Sabitu da Ka’abu ɗan Zubairu da Abdullahi ɗan Rawaha.

A ƙasar Hausa kuwa, mutanen da ake tunanin su suka fara tsara yabon Annabi (SAW) a waƙe tun a ƙarni na 13 zuwa na 17 sun haɗa da Wali ɗanmarina da Wali ɗanmasani da Abdullahi Suka da Muhammadu na Birnin Gwari, Yahya (1988).

Shi kuwa yabon Annabi (SAW) da mandiri/bandiri ya samo asali ne daga al’adar Larabawa; ‘yan ɗariƙun sufaye musamman ƙadirawa su suka fara shigowa da kiɗan mandiri ƙasar Hausa a wajejan ƙarni na 15 zuwa na 16, a lokacin da makarantu da zawiyoyi suka yi yawa. Hausawa sun fara rera waƙoƙin Larabawa a zawiyoyi da wuraren maulidi kafin a samu tsirar mawaƙan mandiri na farko-farko a ƙasar Hausa irin su Shehu Usaman ɗanfodiyo da ‘yarsa Nana Asma’u. Waɗannan waƙoƙi su ne: ‘Godiya Ta Ta’ala’ da ‘Tarbiyyar Mata’ da ‘Halin Mutum’, Hiskett (1963) da Bunza (2009).

A farkon ƙarni na 20 kuwa, mawaƙan mandiri irin su Malam Sadiƙu ɗan Sidi da Darul ƙadiriyya su suka ƙarfafa wannan salo na yabon Annabi (SAW) da kiɗan Mandiri, Bunza (2006).

1.1 Waƙa

Waƙa tsararriyar magana ce ta hikima da ake rerawa ba faɗa kurum ba, wadda ke ƙunshe da wani saƙo a cikin zaɓaɓɓun kalmomi waɗanda aka auna domin furucinsu ya yiwu ba tare da tuntuɓe ba, Yahya (1991:3).

2.0 Taƙaitaccen tarihin Auwal Umar ɗangawuna

An haifi Muhammadu Auwal Umar a unguwar Gawuna da ke ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano a shekarar 1976. A wannan unguwar ta Gawuna ya taso kuma ya yi ƙuruciyarsa. Mahaifinsa malam Umar ya rasu tun yana ƙarami wanda hakan ya sa riƙonsa ya koma hannun kakarsa A’ishatu.

Kamar kowane yaro a ƙasar Hausa, an kai ɗangawuna makarantar allo ta malam Babangida, inda ya fara koyon karatun Alƙur’ani mai girma, daga nan sai aka mayar da shi makarantar Islamiya ta Nurul Islam Gawuna, a nan ya ci gaba da karatun addini har zuwa aji shida. A lokacin da yake tsaka da wannan karatu na addini ne aka saka shi a Birgade Primary School. Daga nan kuma sai ya shiga makarantar Aliya, amma bai daɗe ba sai aka mayar da shi Islamic Secondary School da ke ƙofar Ruwa Kano. Yana tsaka da karatu a wannan makarantar ne mahaifinsa ya rasu, wanda wannan ya zama sanadiyyar tsayawar karatunsa na boko na wani lokaci. Daga nan sai ya dunfari karatun addini haiƙan, ya ci gaba da bin malaman zaure yana karatun littattafan addini a hannunsu. Daga cikin malaman da ya yi karatu a wajensu sun haɗa da: Malam ɗanfulani —ya karanta Fiƙihu a wajensa da Malam Sani da Sayyadi Malam Mansur da sauransu. Daga baya da ya samu sukuni sai ya koma makarantar boko, inda ya koma makarantar Aliya ya kammala karatunsa na Secretary a shekarar 2006.

Auwalu Umar ɗangawuna ya fara rubuta ƙasida tun yana makarantar Islamiya a shekarar 1988. Daga nan sai ya ci gaba da sauraren kasa-kasan mawaƙan Annabi (SAW) musamman waƙoƙin Sharif Rabi’u Usaman Baba. Shi da kansa ɗangawuna yana cewa, “Lokacin da na fara rubuta ƙasida ban san wata ƙa’ida ta ƙafiya ba da sauran ƙa’idoji muhimmai, sai a waƙar ‘Garkuwa’ ta Rabii’u Usaman Baba na fahimci ƙafiya.” Wannan waƙa ta Garkuwa ta zama wani sinadari da ya wanke ƙwaƙwalwarsa wajen sanin ƙa’idojin rubutacciyar waƙa. Wannan dalilin ne ya sa ɗangawuna ya nemi a yi masa muƙamin Garkuwar Rabi’u Usaman Baba bayan kafa ƙungiyar sha’irai ta ƙasa mai suna Shu’ara’ul Islam Muddahi Sayyadil Anam.

Har yanzu Auwalu Umar ɗangawuna yana raye kuma yana yabon Annabi (SAW) da salon waƙoƙin mandiri. Yana da ƙungiya ta yabon Annabi (SAW) mai suna Nushda’un Nabiyyi Wal Auliya’. Ana samun sa a ofishinsa da ke Bayan Gidan Hali Biraza, Birgade Kano.

3.0 Zubi da tsari

Zubin waƙa ya ƙunshi yadda marubuci ya kawo baitocin waƙarsa daki-daki; yayin da tsari kuma yana nuna yadda aka tsara ƙafiya da baitoci da ɗangwayen waƙa, Gusau (2007).

Saboda haka waƙar ‘La’ila’ Murabba’a ce, watau ƙwar huɗu (mai ɗangwaye huɗu). Sannan tana da tsarin ƙafiya ciki da waje ko babban amsa-amo na sautin ‘la’ da ƙananan amsa-amo na sautukan da mawaƙin ya ga dama.

3.1 Mabuɗi

An buɗe waƙar ne da salon waƙoƙin ƙarni na 19, wato aka farawa da sunan Allah, wanda a baitin farko na buɗe waƙar ya ke cewa:

Bismikal Lahu ya Allah,

Rabbu sarki gwani Allah,

Ba ni buɗinka ya Allah,

Nai yabo ga ɗaha ɗan Abdallah.

Mawaƙin ya ci gaba da ambaton Allah da kuma faɗin falalar ambatonsa a farkon kowane irin al’amari tun daga wannan baiti na farko har zuwa na 12.

3.2 Adadin baitoci

Babu wani keɓantaccen baiti a cikin waƙar da ke bayyana adadin baitocin waƙar, sai dai an bi diddiginta ta hanyar saurare har aka gano cewa waƙar tana da yawan baitoci ɗari da arba’in da biyu (142).

3.3 Ma’aunin aruli/kari (bahar)

Duk da waƙar tana ɗauke da wasu larurori na al’ada a fagen yanka waƙa, an gano cewa mawaƙin ya yi amfani da karin ‘Mutadarak’ (— ɓ— + — ɓ —) ne wajen rubuta ƙasidar, kamar yadda za mu iya ganin misali a wannan bautin:

Mujtaba sahibas sidƙi,

Nasirul haƙƙi bilhaƙƙi,

So da begenka sun zam haƙƙi,

Naka kaina Rasulullah.

— ɓ— + —ɓ— + ——

3.4 Marufi

Dangawuna ya rufe wannan waƙar ne da bayyana kansa gami da adireshinsa har da lambar wayarsa da za a iya samunsa. Ga yadda ya saƙa baitocin:

ƙarshe yaka mai saurare na, 

Matso na ba ka adireshina, 

Don in ka tashi nema na,

Ba na buƙatar ka sha wahala. 

Ni a Jahar Kano nake garin baiwa,

Garin masoyan mafi kowa,

A ƙaramar Hukumar Nasarawa,

In ka zo ba ka shan wahala. 

Kuma a Birgade za ka same ni,

A Gawuna ban ɓacewa ni,

Rabbi ya yi baiwa a gare ni,

La ƙuwwata wa la haula. 

Auwalu Umar ne ba wani ba,

Garkuwa ga ɗan Usman Baba,

Mai Afirika ya ci gaba,

A fagen yabon Annabin Allah.

ƙarshe zero eight zero ka ji ba,

Sai ka sa uku shida a gaba,

Biyar shida shida takwas a gaba,

Sifili bakwai zan ji ba wahala.

4.0 Jigo

Babban jigon wannan waƙa ta ‘La’ila’ shi ne yabon Annabi (SAW), ta yadda mawaƙin ya yi amfani da salon kambamawa wajen nuna fifikon Annabi Muhammadu a kan sauran annabawa da halittun Allah gabaɗaya. Za a fahimci hakan a wani baiti da yake cewa:

Ni fa ina ta yi don a gaggane,

Cewa fa shi mafifici ne,

A ambiya ya wuce kowanne,

Ba ya shi a ambiya’ul Lah.

Wannan baitin shi ya zama mabuɗi na kawo sauran baitoci masu nuna fifikon Annabi (SAW) kan sauran annabawa. Amma ba a rasa wasu ƙananan jigo a cikin waƙarba, kamar jigon tarihin tashin ƙiyama da jigon ilimantarwa da sauransu.

5.0 Salo

Fasihin sha’irin ya yi amfani da salailai mabambanta a yayin gina wannan ƙasida tasa, musamman babban salon da ya yi shura a kai na aron kalmomin Larabci da salon kambamawa da salon gangara da salon saɓi-zarce da sauransu.

5.1 Salon aron kalmomin Larabci

Wannan waƙa cike take da kalmomi da jumlolin Larabci tun daga kan amshinta da ke cewa ‘La’ ila Allah la’ilaha illal Lah’ har zuwa cikin baitoci da dama na wannan waƙar. Ga misalin baiti ɗaya don tabbatar da abin da ake ikirari:

Ku bari na koma batun garari,

Da za a sha a *yaumul hashari*,

‘Yan uwa sai ku saurari,

Zancen da zan ka *Rasulullah*

5.2 Salon kambamawa

Sha’irin ya yi amfani da balagar harshe wajen kambama darajar Annabi Muhammad (SAW) fiye da kowa, musamman ma annabawa. Ga misali a wani baiti da yake cewa:

Sidi a ɗaukaka ka fi Idrisu,

A kunya ka fi Iliyasu,

Musɗafa Sayyadi mahsusu (makhsus),

Bil izzi bawan Allah.

5.3 Salon gangara

Gangara wani irin salo ne mai nuna yadda mawaƙi ya naƙalci harshensa da iya fitar da ƙafiya a waƙa. Wannan salo yana ƙulla ɗango ne da mai bi masa. Ga misali a cikin waƙar:

Imamai ne Hussain da Hassan,

Da jin sunansu kai ka san,

Sun tattare sirrika na kusan-

Ci zuwa gun Rasulullah.

Idan aka lura, a ƙarshen ɗango na uku sha’irin ya fara ambaton kalmar ‘kusanci’ ya ƙarasa ta a farkon ɗango na huɗu. Wannan salon shi ake kira gangara, kuma yana da yawa a cikin wannan waƙa.

5.4 Salon saɓi-zarce

Saɓi-zarce yana ƙulla baiti da baiti ne —watau idan aka fara wani zance a baitin baya sai a ƙarasa a baiti na gaba. Ga misalin Saɓi-zarce a wannan waƙa ta ‘La’ila’:

Farko za mu haɗu mu dukanninmi,

Mu je ga Adamu babanmu,

Mu ce da shi ya mahaifinmu,

Cece mu ya Annabin Allah.

Adamu sai ya ce idan ba ku manta,

Ba mun yi saɓo da matata,

Bishiyar da anka ce kar mu ci ta,

Mu ci mun yi saɓon Allah.

Idan aka lura da waɗannan baitoci biyu suna da alaƙa da juna. Wannan salo na Saɓi-zarce cike yake a cikin watan wannan waƙa.

6.0 Kammalawa

An yi amfani da maƙurar taƙaitawa wajen fito da abin da aka fahimta bisa doron nazari game da wannan waƙa; yayin da aka fara gabatar da nazarin da kawo asalin samuwar waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAW), sannan aka kawo tarihin sha’irin a taƙaice da zubi da tsarin waƙar da jigo da salailan da ke ƙunshe a cikin wannan bakandamiyar waƙa.

Manazarta

Domin manazarta ko gyara ko ƙarin bayani, za a iya tuntuɓar Manazarcin ta hanyoyi kamar haka:

WhatsApp: 07063828558

Email: [email protected]

Rataye

https://youtu.be/gƙƙgy1rBiTU?si=kɗnMjW4iK8u1wjFJ

Wannan link yana ɗauke da cikakkiyar wannan waƙa ta ‘La’ila’ a shafin sha’irin na manhajar YouTube.

By ukarofi