Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A na sa ran nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta fara fitar da wasiƙun ɗaukar aiki ga ma’aikatan lafiya sama da 1,000, tare da shirin ɗaukar ƙarin ma’aikata 2,000 domin magance ƙarancin ma’aikata a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na farko a sassan jihar.
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana haka a yayin da yake sa ido kan aikin tantance ma’aikata da kwamiti na musamman da ke gudanar da tantance ma’aikatan gwamnati ke yi a ofishinsa.
Ya ce ɗaukar ma’aikatan lafiyar na daga cikin muhimman ƙudurorin gwamnatinsa na tabbatar da ingantaccen tsarin kula da lafiya, rage cunkoso a asibitoci, tare da samar da kulawa mai inganci ga al’ummar jihar.
Haka kuma ya sanar da shirin ɗaukar malamai 2,000, domin cike giɓin da ya samu a makarantu sakamakon ritayar malamai, da kuma ƙarfafa harkar ilimi a matakin firamare da sakandare.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da adalci da gaskiya a dukkan matakan ɗaukar ma’aikatan, tare da ba da fifiko ga ƙwarewa da cancanta.
