
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Shari’a a Jihar Kano ta umarci dukkan masallatan juma’a da ke faɗin jihar da su gaggauta dakatar da kulle hanyoyin al’umma yayin gudanar da sallar juma’a.
Hukumar ta bayar da wannan gargaɗin ne domin tabbatar da kiyaye zaman lafiyar al’umma da kare ‘yancin masu zirga-zirga, tana mai ba za ta lamunci haifar da tsaiko ga zirga-zirga ba a sanadiyyar sallolin jam’i.
Ta kuma yi gargaɗin dukkan wani masallaci da aka samu ya take haramcin, za a gurfanar da shi a kotu domin hakan ya zame wa sauran izina.
A cewarta, duk da cewa sallar Juma’a ɗaya ce daga cikin wajiban addinin Musulunci, wajibi ne a gudanar da ita ta yadda ba za ta kawo cikas ga zirga-zirga ba, jefa rayukan jama’a cikin haɗari ko tauye ‘yancin wasu.
Masu sharhi sun bayyana unarnin a matsayin “ci-gaba mai amfani kuma matakin da ya zama wajibi”, domin tare hanyoyin da al’umma ke yi da sunan ibada ya saɓa wa karantarwar addinin Musulunci wanda ya ginu ne akan tsari, la’akari da girmamawa ga ‘yancin wasu.
Haka kuma sun yi kira da a yaɗa saƙon sosai ta yadda al’umma da dama za su faɗa kuma su kiyaye umarnin, duba da muhimmancin gudanar da ayyukan addini ba tare da takura wa ɗaiɗaikun mutane ba.
Ana sa ran wannan umarni ya magance matsalolin da suka jima suna damun mutane musamman masu ababen hawa da ke fuskantar cinkoso da hana su wucewa ta manyan titina a yayin sallar juma’a.
