Matsalar ‘network’ ce – Akpabio ya yi magana kan tura sakamakon zaɓe a sabuwar doka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar ba ta ƙi amince wa tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba, saidai ta tsaya ne akan hukuncin da ke cikin kundin dokar zaɓe na 2022.

Akpabio ya faɗi haka ne jiya Asabar a Abuja a lokacin da yake jawabi a taron ƙaddamar wani littafi da ke magana akan nauye-nauyen da ke kan ‘yan majalisa a Nijeriya.

Ya bayyana cewa, tura sakamakon zaɓe ta na’ura har yanzu yana bisa doka, saidai an cire kalamar “real time” daga cikin bayanin da sakin layin ya ƙunsa.

Ya ce, an ɗauki matakin ne domin ba Hukumar Zaɓe (INEC) damar yanke hukuncin tsarin da ya dace da tura sakamako, saboda la’akari da ƙalubalen fasaha da tsaro.

Shugaban majalisar dattawan ya ƙara da cewa majalisarsu za ta cigaba da ƙoƙarin samar da dokar da za ta zama masalaha da buƙatun ‘yan Nijeriya.

Da yake tsokaci akan al’amarin, tsohon shugaban majalisar, David Mark, ya ce ya dace majalisar dokoki ta ƙasa ta ƙyale INEC ta yanke hukuncin karɓar sakamako ta na’ura ko kuma akasin haka.

Ya ƙara da cewa, Jam’iyyar ADC, wadda ɗanta ne shi a yanzu, tana goyon bayan aika sakamakon ta na’ura ɗari bisa ɗari.

A makon da ya gabata ne ƙudirin dokar gyaran zaɓe ya tsallake karatu na uku a majalisar, inda ta ƙi amincewa da mayar da tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura wajibi a dokance, lamarin da haddasa cece-kucen acikin masana da al’ummar ƙasa.

By Babaji