Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sake ganawa da Fubara da Wike a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Litinin Shugaba Bola Tinubu ya gana da Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas a matsayin wani ɓangare na warware rikicin siyasar da ke tsakanin mutanen biyu.

An ruwaito cewa, wasu jagororin siyasa daga jihar sun samu halartar zaman, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Saidai ba a bayyana abin da zaman nasu ya ƙunsa ba a lokacin haɗa wannan rahoto.

Zaman, wanda aka yi ta bayan fage na zuwa ne yayin da wani sabon rikicin siyasa ke shirin kunno kai a Ribas, wanda ya ƙunshi manyan masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.

A cewar jaridar The Nation, majiyoyi da ke kusa da al’amarin sun ce tattaunawar zaman ta ginu ne akan al’amuran da suka shafi jihar, duk da cewa babu wani jawabi a hukumance game da hakan.

Wata majiya ta ce bayan zaman, Gwamna Fubara ya raka Wike zuwa gidansa da ke Guzape a Abuja.

Haka kuma, majiyar ta yi ikirarin cewa gwamnan ya yi wa Wiken magiya cewa su cigaba da mutunta juna a alaƙarsu, inda ya yi masa alƙawarin ba zai sake masa rashin ɗa’a ba.

By Babaji