Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta Jihar Zamfara (Islamic Future Guidance Initiative (TIFGI), ta bayyana goyon bayanta ga ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru da Bungudu Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bungudu) a matsayin ɗan takarar gwamna a shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.
Shugaban ƙungiyar Malam Rabiu Yahaya ya bayyana hakan a taron manema labarai yau Alhamis a Gusau.
A cewar sa, ƙungiyar ta tabbatar da Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu a matsayin ɗan takarar da yafi cancanta, yana mai kira ga shugabannin jam’iyyar ta APC da suka hada da Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura,Sanata Abdulaziz Yari da Kuma ƙaramin ministan tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle da su jajirce wajen shawo kan matsalolin rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar don kaucewa sake faruwar matsalar jam’iyyar da ya faru a shekarar 2019.
A cewar sa, Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu, shine kawai za a tsayar ɗan takarar gwamna a shekarar 2027 in har ana so Jam’iyyar APC tayi nasara a Jihar.
“Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu, yayi ƙoƙari matuƙa wajen inganta rayuwar alummar Jihar Zamfara, Kuma mun lura shine kawai za a tsayar ɗan takarar gwamna idan har a na so jam’iyyar APC ta yi nasara a 2027 a Zamfara.’
Malam Rabiu Yahaya ya ƙara da cewar matakin da ƙungiyar su ta ɗauka abun lura ne, duba da halin da jam’iyyar APC take ciki a yanzu na samun rashin haɗin kai a tsakanin jagororin ta.
Malam Rabiu Yahaya, ya yi nuni da cewa, idan har Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura, Sanata Abdulaziz Yari da karamin ministan tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle ba su sanya hannu wajen kawo ƙarshen matsalar jam’iyyar ba, abinda ya faru a shekarar 2019 tarihi zai maimaita kansa a 2027.
“Muna kira ga jagororin jam’iyyar APC da masu faɗa aji cewar su maida hankali wajen fidda ɗan takarar da yafi cancanta musamman Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu tare da tabbatar da an samu haɗin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar da magoya bayan ta, don samun nasarar jam’iyyar APC a Jihar Zamfara a zaɓen da ke tafe”.
Haka zalika, Malam Rabiu Yahaya, ya bayyana cewar ƙungiyar su ta Malaman Tsangaya za su cigaba da faɗakar da alumma musamman magoya bayan Jam’iyyar APC a jihar wajen ganin an tsai da ɗan takarar da yafi cancanta don samun nasarar jam’iyyar a shekarar 2027.
