Amurka ta tura wa Nijeriya jiragen yaƙi, makamai da sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla jiragen yaƙin sojojin Amurka guda uku ne suka sauka a Nijeriya daga ranar Alhamis zuwa Juma’a.

Wannan shi ne rukunin farko na sojoji da jiragen Amurkan da suka sauka a arewa maso gabashin ƙasar domin fara haɗin gwiwar farmaki kan ‘yan ta’addan ISWAP tsakanin Amurka da Nijeriya.

Jaridar TheNewYork Times ta rawaito cewa wani jirgin sojan Amurka ya sauka a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a daren Alhamis, yayin da ake sauke kayan aiki daga wasu jirage da suka iso.

Kamfanin Reuters ya ce Amurka za ta tura sojoji 200 domin horas da rundunar sojin Nijeriya, tare da ƙara wa wasu jami’an Amurka da ke ƙasar ƙarfi.

Wannan mataki na zuwa ne bayan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

A makon da ya gabata ne kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka ya ziyarci Abuja inda ya gana da Shugaba Bola Tinubu da manyan jami’an tsaron Nijeriya akan al’amarin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

Jami’an Amurka sun ce, sabbin sojojin za su mayar da hankali ne akan tattara bayanan sirri da kuma tallafa wa sojojin Nijeriyar a yaƙi da ta’addanci da ya jima yana addabar ƙasar.

By Babaji