Hukumar DSS za ta gurfanar da El-Rufa’i a kotu kan saɓa wa dokokin tsaron ƙasa

Spread the love

Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar 25 ga Fabrairu bisa zargin aikata laifukan yanar gizo da kuma karya tsaron ƙasa.

Hukumar tsaron ta zargi El-Rufai da karya Dokar Hana Laifukan Yanar Gizo ta 2024 (Cybercrimes Prohibition Act, 2024) da kuma Dokar Sadarwa ta Najeriya ta 2003 (Nigerian Communications Act, 2003).

A tuhuma ta farko, an zargi El-Rufai da cewa a ranar 13 ga Fabrairu, yayin hirarsa a shirin Prime Time na tashar Arise TV a Abuja, ya amsa a cikin tattaunawar cewa shi da wasu abokan aikinsa sun yi kutse tare da sauraren wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Ribadu, ba bisa ƙa’ida ba.

An ce laifin ya saɓa wa kuma yana ƙarƙashin hukuncin Sashe na 12(1) na Dokar Cybercrimes (Prohibition, Prevention, da sauransu) Gyaran 2024.

A tuhuma ta biyu, an zargi tsohon gwamnan da cewa a ranar 13 ga Fabrairu, yayin hirarsa a shirin Prime Time na Arise TV a Abuja, ya bayyana cewa ya san kuma yana hulɗa da wani mutum da ya yi kutse tare da sauraren wayar NSA ba bisa ƙa’ida ba, amma bai kai rahoton mutumin ga hukumomin tsaro da suka dace ba.

An ce laifin ya saɓa wa doka, kuma yana ƙarƙashin hukuncin Sashe na 27(b) na Dokar Cybercrimes (Prohibition, Prevention, da sauransu) Gyaran 2024.

A tuhuma ta uku kuwa, an zargi El-Rufai da wasu da har yanzu ba a kama ba da cewa a wani lokaci a shekarar 2026 a Abuja, sun yi amfani da wasu na’urori ko tsarin fasaha da suka jefa lafiyar jama’a da tsaron ƙasa cikin haɗari, tare da haifar da fargabar rashin tsaro a tsakanin ’yan Najeriya ta hanyar yin kutse da sauraren wayar NSA ba bisa ƙa’ida ba.

DSS ta ce wannan aikin, wanda tsohon gwamnan ya amince da shi yayin hirarsa a ranar 13 ga Fabrairu a shirin Prime Time na Arise TV a Abuja, laifi ne da ya saɓa wa doka, kuma yana ƙarƙashin hukuncin Sashe na 131(2) na Dokar Sadarwa ta Najeriya ta 2003.

By Babaji