Kungiyoyin ƙwallon ƙafar Italiya na cikin wani yanayi mai matuƙar muni a gasar Champions League, inda akwai yiwuwar babu ko ɗaya daga Serie A da za ta kai zagayen na biyu wato na ’yan 16 a bana.
Tun bayan dawo da tsarin zagayen ’yan 16 a kakar 2003-04, a ko da yaushe akwai aƙalla wakili guda daga Italiya.
A lokuta 12 cikin shekaru 22 da suka wuce ma har ƙungiya uku ne suka kai wa wannan mataki.
Ba a taɓa samun kakar da babu ko ɗaya ba daga mai buga Serie A tun 1987-88, lokacin da Napoli ta fita a zagayen farko na European Cup a hannun Real Madrid.
A kakar bana Inter Milan ta yi ban kwana da gasar, sakamakon da Bodo/Glimt ta yi waje da ita, wasan da ya bayar da mamaki.
Inter ta fara rashin nasara 3-1 a wasan farko, sannan aka doke ta 2-1 a San Siro, kenan an yi mata 5-2 gida waje kenan.
Wannan ne karo na farko da Inter ta fita daga Champions League a hannun ƙungiya ba daga manyan lig-lig biyar na Turai ba, wato Ingila ko Sifaniya ko Jamus ko Italiya ko kuma ta Faransa.
Yanzu dai Juventus, wadda aka ci 5-2 a wasan farko a Galatasaray – ta karɓi baƙuncin wasa na biyu ranar Laraba, inda ta sake cin 3-2.
Idan aungiyoyin biyu suka kasa kai wa zagaye na biyu, zai zama tarihi mafi muni da ba wata daga Serie A a zagaye na biyu a Champions League cikin shekara 40.
Wannan lamarin zai rage martabar Serie A a Turai da hasarar samun kuɗin shiga da karin matsin lamba ga kociyoyi da shugabanni, sannan za a iya rage ƙungiyoyin da za su shiga babbar gasar tamaula ta Champions League a baɗi.
