Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya gwangwaje limana jihar da kyautar sabbin motoci a ƙarshen makon jiya.
Da yake gabatar da motocin Lawal ya ce ya yi haka ne domin tallafawa limaman a aikinsu na yada addinin Musulunci a faɗin jihar.
Ya ce jihar Zamfara na daga cikin jihohin ƙasar nan da aka gina ta da addinin Musulunci sannan limamai da dama ke gina mutane bisa addinin a ƙananan hukumomi 14 dake jihar.
Lawal ya ce tallafawa wa limamai haƙƙi ne dake lafaɗun gwamnati da ya zama dole ta sauke.
“Mun gina masallatai da gidaje domin limamai sannan a gani na ya kamata mu samar musu da ababen hawa domin tallafawa wa aikin da suke yi.
“Iya yin tafiya ba tare da takura ba na da mahimmanci musamman wajen yada adinin musulunci.
“A dalilin haka ya sa muka zaɓi limamai 40 domin ganin suna yin tafiya ba tare da takura ba.
Gwamnan ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafawa limaman musamman yadda yanzu shine karo na farko da gwamnatin ke kyautar motoci wa limamai a jihar.
Ya yi kira ga limaman da su ci gaba da yin addu’o’i domin samar da zaman lafiya a jihar da Nijeriya gaba ɗaya.
Mashawarcin gwamnan kan harkokin addini Sheikh Bello Almufty ya kwatanta Gwamna Lawal a matsayin gwamna mai gaskiya, adalci da samar da ci gaba.
Ya ce gwamnatin Lawal ta inganta rayuwar limamai musamman ta hanyar inganta walwalan su a jihar.
