Daga DAUDA USMAN
An shawarci al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma sauran sassan duniya da su ƙara himma wajen aiwatar da ayyukan alheri a cikin wannan watan azumin Ramadan mai tsarki.
Wannan kira ya fito ne daga wani fitaccen ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Mustapha Mairoba, wanda aka sani a matsayin jigo a kasuwar ƙofar Wambai da ke cikin birnin Kano, kuma na hannun daman marigayi Sheikh Malam Ibrahim Shehu Dahiru Usman Bauchi a Kano.
Haka kuma shi ne shugaban ƙungiyar Dattawan Kasuwar ƙofar Wambai da kewayenta.
Ya bayar da wannan shawara ne yayin wani taron walimar buɗa baki da ya shirya a harabar ƙofar gidansa da ke Kano a ranar Juma’ar da ta gabata.
Alhaji Mustapha Mairoba ya bayyana cewa, la’akari da irin ƙalubale da fitintinu da suke addabar ƙasar nan, ya dace Musulmi su ƙara yawaita addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya baki ɗaya. Ya ce wajibi ne a nemi gafarar Ubangiji kan kura-kurai da miyagun ayyukan da wasu ke aikatawa, tare da komawa kan tafarkin gaskiya.
Ya kuma jawo hankalin waɗanda suka san suna aikata munanan ɗabi’u da su yi amfani da wannan wata mai tsarki wajen gyara halayensu, su maye gurbin munanan ayyuka da nagari, domin neman yardar Allah da samun zaman lafiya a jihar Kano da Nijeriya gaba ɗaya.
Haka zalika, ya yi kira ga ‘yan kasuwar ƙofar Wambai da sauran ‘yan kasuwannin cikin birnin Kano da ma kasa baki ɗaya, musamman masu sayar da kayan abinci da ake amfani da su wajen sahur da buɗa baki, da su ji tsoron Allah su kuma sauƙaƙa wa jama’a ta hanyar rangwame da taimakon marasa ƙarfi a wannan wata mai albarka.
Bugu da ƙari, ya jajanta wa ‘yan kasuwar Singa da gobara ta shafa a Kano, wadda ta haddasa asarar kayayyaki na maƙudan kuɗaɗe. Ya yi musu addu’ar Allah Ya mayar musu da mafificin abin da suka rasa.
A ƙarshe, Alhaji Mustapha Mairoba ya yi fatan alheri ga al’ummar Musulmi, tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon kammala ibadun wannan watan Ramadan lafiya da samun lada mai yawa.
