Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministar Harkokin Kuɗi ta ƙasa, Dakta Doris Uzoka-Anite, wadda kuma ita ce Shugabar Kwamitin Raba Kuɗin Tarayya (FAAC), ta yaba wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa sabuwar dokar zartarwa da ya sanya, tana mai cewa matakin zai ƙara ƙarfin kuɗaɗen da ke shiga Asusun Tarayya.
Da take jawabi ga mambobin FAAC a Abuja ranar Juma’a, ministar ta bayyana cewa umarnin shugaban ƙasa ya tanadi a riƙa tura wasu muhimman kuɗaɗen da ake samu daga ɓangaren mai da iskar gas kai tsaye zuwa Asusun Tarayya, maimakon tsarin da ake riƙe wani ɓangare a baya.
A cewarta, wannan zai tabbatar da tsari, gaskiya da kuma kare kuɗaɗen man fetur daga duk wata tangarɗa.
Uzoka-Anite ta bayyana matakin a matsayin gyaran tsarin kuɗi na ƙasa da zai dawo da bin ƙa’idojin kundin tsarin mulki wajen tafiyar da kuɗaɗen man fetur, tare da ƙara yawan kuɗaɗen da ake rabawa tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Ta ce hasashen kuɗaɗen shiga na kara inganta sakamakon sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da su, musamman a ɓangaren gyaran haraji da ke faɗaɗa tushen haraji, ƙara biyayya ga doka da inganta tsarin tattara kuɗace.
Ministar ta yi ƙarin haske cewa umarnin na ranar 13 ga Fabrairu ya dakatar da ware kashi 30 cikin 100 ga Asusun Binciken Sabbin Rijiyoyin Mai (Frontier Eɗploration Fund), tare da dakatar da kashi 30 cikin 100 na kuɗin kula da riba da ake biya wa NNPC daga ribar mai da gas.
Haka kuma, an umurci a riƙa tura tarar da ake karɓa kan ƙonewar iskar gas (gas flare penalties) zuwa Asusun Tarayya, tare da haramta duk wata cire kuɗi da ba ta dace da kundin tsarin mulki ba kafin a tura kuɗaɗen.
A cewarta, wannan gyara ya sauya tsarin “riƙe kuɗi a gaba” zuwa sabon tsarin “tura duka zuwa Asusun Tarayya da farko,” wanda hakan zai tabbatar da cewa ƙarin ribar mai da gas za ta riƙa shiga kai tsaye cikin asusun da ake rabawa.
Ta ce hakan na nufin ƙarin kuɗaɗe a duk wata, wanda zai amfanar da dukkan matakan gwamnati.
Sai dai ministar ta yi gargaɗin cewa karin kuɗaɗe ba ya nufin a yi sakaci. Ta ce idan aka saki maƙudan kuɗaɗe lokaci guda, hakan na iya ƙara hauhawar farashi, matsin lamba kan canjin kuɗi da kuma rage ƙarfin sayen kuɗin da aka raba. Don haka ta ba da shawarar a riƙa sakin duk wani ƙarin kuɗi a hankali, tare da adana wani ɓangare a matsayin tanadi domin daidaita kasafin kuɗi a watannin da kuɗaɗen shiga suka ragu.
Ta kuma ba da shawarar a ƙarfafa haɗin gwiwa da Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin daidaita shigar kuɗaɗe cikin tattalin arziki da manufofin kula da yawan kuɗi a kasuwa.
Uzoka-Anite ta buƙaci jihohi da ma’aikatu su mayar da hankali kan kashe kuɗaɗe a ayyukan raya ƙasa maimakon faɗaɗa kashe-kashen yau da kullum, tana mai jaddada cewa saka jari a ababen more rayuwa, noma, makamashi da sauran ɓangarori masu samar da arziki zai taimaka rage matsin hauhawar farashi.
A ƙarshe, ta sanar da shirin ɓullo da rahotannin bayyananniyar kuɗaɗen shiga a kowane wata, tare da cikakken bayani kan kuɗaɗen da aka samu sakamakon gyaran haraji da umarnin shugaban ƙasa.
