Al Green ya ƙalubalance Trump kan bidiyon Obama

Spread the love

Dan majalisar Democrat Al Green ya bayyana cewa ya ƙalubalance Shugaban Amurka, Donald Trump, a jawabin State of the Union kan bidiyo “mai tsananin rashin kunya” da aka wallafa a kafafen sada zumunta na Trump, wanda ke nuna tsohon Shugaba Barack Obama da matarsa a matsayin apes.

Green, daga Teɗas, ya nuna takarda mai rubutu: “Black people aren’t apes,” yayin da Trump ke shiga ɗakin Majalisar. White House ta cire bidiyon daga kafafen sada zumunta, Trump ya ce wani ma’aikaci ne ya wallafa shi.

“Ina so ya san cewa nuna Shugaba Obama da matar sa a matsayin apes ba abu ne da za mu aminta da shi ba, abin kunya ne, kuma ba za mu amince da hakan ba,” inji Green.

Green ya bayyana cewa ya zauna a kujerar gefen dandalin da Trump zai bi kafin ya hau dandalin jawabi. Wannan shekara ta biyu kenan da aka fitar da shi daga Majalisar saboda nuna rashin jituwa da Trump.

By ukarofi