‎Saulawa ne sabon shugaban APC a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Dakta Gambo Saulawa wanda tsohon kwamishinan albarkatun ruwa ne ya maye gurbin tsohon shugaban jam’iyar malam Sani Aliyu Daura wanda ya sami muƙamin kwamishina.

Haka kuma ya biyo bayan gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyar APC a matakin jihar ta hanyar sasanci.

Alhaji Bala Abubakar Musawa ya sake komawa a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar a karo na biyu.

Zaɓen ya samu shedar jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, da kwamitin shirya zaɓe daga uwar jam’iyyar APC ta ƙasa.

Haka kuma, an zaɓi Alhaji Yahaya Idris Asasanta a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Katsina, Alhaji Sama’ila Sabuwar Kasa mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Funtua, Hon. Musa Maikudi Kankia mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyar Daura.

Kazalika, an zaɓi Hon. Adnan na Habu tsohon kwamishina a matsayin sakataren jam’iyyar, Hon. Hassan Na Kawari a matsayin ma’ajin jam’iyyar, Alhaji Mamman Yaro Batsari a matsayin mai binciken kuɗi na jam’iyyar.

Sai kuma, Alhaji Ahmed Hassan Mashi a matsayin sakataren tsare, tsare na jam’iyyar, Shehu Kabir Jani sakataren walwala da jin daɗi, Hajiya Aisha Yahaya shugabar mata ta jam’iyyar, da dai sauran su.

A jawabin sa bayan ƙaddamar da sabin shugabannin jam’iyar Dr. Bishir Gambo Saulawa ya gode ma Allah da ya zama shugaban jam’iyyar, wanda ya nuna ranar a matsayin rana mai matuƙar muhimmanci da kuma tarihi a rayuwar sa.

Ya yi godiya ga ya’yan da su ka ga dacewar sa ya shugabanci jam’iyyar tun daga gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa, tsohon Gwamna Aminu Bello Masari, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC.

Sabon shugaban jam’iyar ya tabbatar ma shugabanni da yan jam’iyyar APC cewa, zai zama mai adalci da tsare mutuncin dukkan ya’yan jam’iyyar tun daga matakin mazaɓa, ƙaramar hukuma da jiha.

Shi ma a jawabin sa, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa, ya zama dole duk ɗan jam’iyyar APC ya yi ma shuwagabanninta biyayya.

Ya jaddada cewa, shi kansa biyayya ya ke ga jam’iyya domin ita ce uwa, kuma zai ci gaba da yin biyayya a gare ta domin duk mai biyayya shi ke cikin nasara a rayuwa.

Gwamnan ya ce a yanzu jihar Katsina babu sauran ‘yan adawa domin haka yayi kira ga al’ummar jihar da su fito gaba ɗaya in lokacin zaɓe yayi su zaɓi Bola Tinubu da Dikko Raɗɗa.

By ukarofi