Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Sarkin Sarakunan Kasuwannin Kano, Alhaji Isa Abba Ibrahim, ya bayyana cewa daina yin wasu ayyukan alheri a masallatai, musamman umarnin yin salati bayan sallar jam’i, na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalolin da al’umma ke fuskanta a yau.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin wata addu’a da aka gudanar a fadarsa da ke kasuwar Singa a Kano, inda ‘yan kasuwa suka taru domin yin addu’ar neman zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Ya ce a baya, musamman shekaru 20 zuwa 40 da suka wuce, limaman masallatai kan buƙaci jama’a su yi salati bayan sallar jam’i, wanda a cewarsa wani muhimmin aiki ne na ibada da ke ƙara samun albarka a cikin al’umma.
Sai dai ya nuna damuwa cewa a yanzu irin wannan ɗabi’a ta ragu a wasu masallatai, lamarin da ya ce ya kamata a sake duba shi domin dawo da al’adun ibada da suka saba.
Sarkin ya yi misali da cewa idan aka yi la’akari da masallatai goma a wata unguwa, inda a kowanne masallaci mutane goma ke halartar sallar jam’i, kuma aka yi salloli biyar a rana, to idan aka buƙaci kowanne mutum ya yi salati sau goma, hakan zai haifar da dubban salati da ake yi wa Manzon Allah (SAW) a rana guda.
A cewarsa, irin wadannan ayyuka na ibada suna taimakawa wajen kawo albarka da zaman lafiya a cikin al’umma.
A ƙarshe, Alhaji Isa Abba Ibrahim ya yabawa ‘yan kasuwa bisa hadin kan da suka nuna wajen shirya addu’ar, tare da kira gare su da su ci gaba da rike gaskiya, rikon amana, da kauce wa hassada, domin ci gaban kasuwanci da zaman lafiya a al’umma.
Haka kuma ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa kokarinta na bunkasa harkokin kasuwanci ta hanyar ayyukan raya kasa da inganta tituna a kasuwanni.
Sarkin ya kuma yaba wa Masarautar Kano da Hakimin Fagge kan irin goyon baya da hadin kai da suke bai wa ‘yan kasuwa a kowane lokaci domin bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
