Gobara ta ƙone wani sashen Ma’aikatar Ma’aikata a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar yau Litinin ne wani sashe na ofishin Ma’aikatar Ma’aikatan Tarayya ya kama da wuta, lamarin da ya jefa ma’aikata da masu ziyara cikin firgici a ginin gwamnatin da ke Abuja.

Al’amarin ya faru ne a sashen da ofisoshin ma’aikatar suke.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a gano musabbabin faruwar al’amarin ba a hukumance.

Tuni dai masu bayar da agajin gaggawa sika hallara a yankin don kashe gobarar da kokowa Haan cigaba da yaɗuwarta.

Ana sa ran hukumomi za su gudanar da nazarin na musamman akan matakin damejin da iftila’in ya haifar da zarar an kammala kashe wutar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a samu wani bayani akan jikkata ko matakin ɓarnar gobarar ba.

By Babaji