Eid-Al-Fitr: Sarkin Musulmi ya umarci a fara duba jinjirin watan Shawwal daga Laraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya yi kira ga al’ummar Musulmi a fadin Nijeriya da su fara neman jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadana da kuma shigowar bikin Sallah ƙarama, wato Eid-el-Fitr.

Sanarwar ta fito ne ta hannun Sambo Wali Junaidu a madadin Majalisar Masarautar Sarkin da ke Sakkwato.

A cewar sanarwar, ranar Laraba 18 ga Maris, 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga Ramadan 1447AH ita ce aka ware domin duban jinjirin watan.

Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci, ya nemi dukkan wanda ya ga jinjirin wata da ya sanar da hakimin yankinsa ko shugaban ƙauye domin isar da saƙo ga hukumomi domin tabbatarwa.

Haka kuma, an samar da lambobin waya na musamman domin saukaka kai rahoton sahihin ganin jinjirin wata kai tsaye zuwa ofishin Sarkin Musulmi.

Za a sanar da ranar Sallah a hukumance ne bayan tabbatar da ganin jinjirin wata bisa ka’idojin addinin Musulunci kamar yadda aka saba.

By Babaji