Kwankwaso na shirin barin NNPP don koma wa ADC bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da babban zaɓen 2027 ke cigaba da ƙaratowa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin koma wa jam’iyyar adawa ta ADC.

Kwankwaso ya ɗauki wannan matakin ne yayin da ya wakilta Buba Galadima ya fara tattaunawa da jagororin ADC.

Hakan na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na kwanan nan, wanda ya jaddada jagorancin ADC ga tsagin da ke ƙarƙashin Agbo Major akan Ajuji Ahmed, wanda na hannun daman Kwankwaso ne.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa, Kwankwaso na dab da shiga ADC musamman bisa la’akari da yadda wasu jiga-jigan jam’iyyar ke kai masa ziyara a ‘yan kwanakin nan.

A cewarsu, zuwa yanzu babu wata yarjejeniya da aka ƙulla game da tsare-tsaren jam’iyyar. Saidai, ana sa ran ADC za ta gudanar da babban taro da zai ƙunshi dukkan ‘yan takara da kuma yin zaɓukan fidda gwani da za a dama da kowane ɓangare, wanda ana ganin ya ci karo da tsarin Kwankwaso na zaɓar ɗan takara bisa yarjejeniya.

By Babaji