Daga JOHN D WADA a Keffi
Muƙaddashin daraktar cibiyar karatun jinsi (Ag. Director, Centre for Gender Studies) a babbar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Dr. Comfort Adokwe, ta sanar cewa kashi 70 na ɗalibai mata da kuma kashi 30 na ɗalibai maza suna fuskantar matsalar cin zarafi ta jinsinsu a manyan makarantun ƙasar nan.
Ta bayyana haka ne a lokacin da take ganawa da manema labarai jim kaɗan kafin a fara bikin Ranar Mata ta Duniya na shekarar 2026, wanda cibiyar ta shirya a ranar Litinin na wannan mako a jami’ar da ke Keffi.
Ta ce wani bincike na musamman da wata cibiyar bincike mai suna National Campus Climate Baseline Survey on Sexual Harassment in Tertiary Institutions in Nigeria, tare da haɗin gwiwar Alliances for Africa da cibiyoyin karatun jinsi, a wasu jami’o’in Najeriya guda 12, ya tabbatar da hakan a kwanakin baya.
A cewar Dr. Comfort Adokwe, binciken na da alaƙa da wani shirin shekaru biyar da wata cibiya mai suna Co-Impact ke tallafawa, wanda ke da manufar tunkarar matsalar cin zarafin ɗalibai mata da maza ta jinsinsu, tare da ƙarfafa ƙoƙarin kawo ƙarshen lamarin a jami’o’in ƙasar nan baki ɗaya.
Muƙaddashin daraktar ta ci gaba da cewa, “An gudanar da binciken ne a wasu manyan jami’o’in ƙasar nan guda 12 da ke wakiltar dukkan shiyyoyi shida na Najeriya, inda aka tattara ra’ayoyin ɗalibai da ma’aikata sama da 4000, ciki har da malamai da waɗanda ba malamai ba.
“Binciken ya nuna cewa cikin kashi 70 na ɗalibai mata da kashi 30 na takwarorinsu maza sun fuskanci cin zarafi ta jinsinsu a manyan jami’o’i.
“A cikin ma’aikatan jami’o’in kuma, kimanin kashi 63 na mata da kashi 37 na maza suna fuskantar matsalar cin zarafin a jami’o’i.”
Dr. Adokwe ta ƙara da cewa, “A cibiyar mu ta karatun jinsi a nan Jami’ar Jihar Nasarawa, mun ƙuduri aniyar ci gaba da wayar da kai da tallafawa shirye-shiryen da ke kare haƙoƙin ɗalibai, musamman ‘ya mace, tare da ƙarfafa duk wani mataki na tunkarar wannan matsala ta cin zarafi.
“Muna kuma yaba wa Alliances for Africa da sauran abokan aiki dangane da samar da ingantattun tsare-tsare domin shawo kan matsalar a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.
“A yayin da muke bikin Ranar Mata ta Duniya, muna kira ga hukumomin jami’o’i daban-daban, masu ƙirƙiro tsare-tsare, ɗalibai da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da su haɗa hannu wajen tabbatar da cewa manyan makarantunmu sun zama wurare masu tsaro da kwanciyar hankali ga kowa,” in ji ta.
Suma manyan baƙi na musamman da suka halarci taron daga bisani, ciki har da Shugabar Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman; Kwamishinar Hukumar Federal Character Commission, Hon. Halima Jabiru; da wakilin Sarkin Keffi, Dr. Shehu Chindo Yamusa, da sauransu, duk sun yi kira na musamman da a riƙa tabbatar da dama da haƙoƙin ‘ya mace domin ba ta damar cimma cikakken burinta na rayuwa, musamman a ɓangaren ilimin zamani da na addini.
