Zulum ya ziyarci Ngoshe, ya yi alƙawarin sake gina ababen more rayuwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara garin Ngoshe da ke kusan kilomita 40 daga Gwoza domin duba irin ɓarnar da hare-haren Boko Haram suka yi a yankin.

Zulum, wanda ya fara rangaɗdin kwana biyu domin ƙarfafa gwiwa da jajenta wa waɗanda hare-haren suka shafa a Ngoshe da Pulka, ya kuma raba kuɗaɗe da kayayyakin tallafi ga sama da mutane 30,000 da lamarin ya shafa.

Da yake zantawa da manema labarai bayan duba yankin, gwamnan ya bayyana barnar da aka yi a matsayin mai girgiza zuciya da matuƙar tayar da hankali.

“Abin takaici ne ganin irin wannan barna. A ‘yan kwanakin nan ban taba ganin irin haka ba. Amma Insha Allah, za mu sake gina komai fiye da yadda yake a da,” inji Zulum.

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati za ta sake gina gidaje da muhimman ababen more rayuwa da aka lalata, tare da kara kaimi wajen inganta tsaro domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Gwamnan ya ce ya umurci Ma’aikatar Sake Gina da Farfado da Yankunan da Bala’i ya shafa da su gaggauta tantance asarar da aka yi domin fara aikin gyara duk gine-ginen da aka kona.

Haka kuma, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayar da tallafi ga rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force domin ƙarfafa ayyukan soji a yankin.

Zulum ya jaddada cewa tsaunukan Mandara na daga cikin manyan maboyar ‘yan ta’adda, yana mai cewa dole ne a kai musu farmaki kai tsaye domin kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Ya yaba wa kokarin rundunar soji, musamman kwamandan rundunar ta 7 Diɓision da Brigade Commander, bisa yadda suka kara ƙarfafa tsaro a Ngoshe, yana mai cewa an ƙara yawan sojoji a yankin har sau biyu.

A wani ɓangare, gwamnan ya sha alwashin cewa Ngoshe ba za ta sake faɗawa hannun ‘yan ta’adda ba, yana mai jaddada muhimmancin garin ga tsaron yankin baki ɗaya.

“Ngoshe na da matukar muhimmanci. Idan ta faɗi, zai shafi Pulka, Kirawa, Gwoza har ma da Bama. Ba za mu bari hakan ta faru ba,” inji shi.

Zulum ya samu rakiyar Sanata Mohammed Ali Ndume da dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Gwoza, Hon. Abdullahi Buba Abatcha, da kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati a yayin ziyarar.

By ukarofi