Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗaliban sun haɗa da Abdullahi da Sani Matori da Abubakar Abdullahi sai malamin su Yazid Ahmed,sun samu matsayi na biyu a gaba ɗaya inda suka fafata da ɗalibai daga ƙasashen duniya.
GwamnanJihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya taya waɗannan haziƙan ɗalibai biyu na Government College Funtua murna bisa gagarumar nasarar da suka samu a Gasar I-FEST² ta ayyukan bincike ta shekarar 2026, wadda Association for the Future of Sciences and Technology ta shirya a ƙasar Tunisiya.
Gwamnan ya bayyana farin cikinsa ganin yadda ɗaliban Jihar Katsina ke fafatawa tare da samun nasara a matakin duniya.
Ya ce: “Wannan nasara na nuna cewa gyaran da muke yi a fannin ilimi yana haifar da sakamako mai kyau. Matasa namu suna da baiwa da ƙirƙira da za su iya fafatawa da mafi ƙwarewa a duniya.”inji Dikko.
Haka kuma, ya yaba wa ɗaliban bisa yadda suka ɗaukaka sunan Jihar Katsina da Najeriya a wannan gagarumar gasa ta duniya.
Gasar I-FEST² ta 2026 ta haɗa ɗalibai sama da 1,200 tare da ayyuka 450 daga ƙasashe 40 a ƙasar Tunisiya.
Wannan babbar gasa, wadda aka shirya karo na 17 ta hannun ƙungiyar ATAST, ta nuna ƙwarewar matasa a fannonin kimiyya, fasaha da ƙirƙira daga sassa daban-daban na duniya.
Gwamna Radda ya ƙara da cewa: “Lokacin da muka zuba jari a ilimi, muka tallafa wa dalibai da malamai, muna samar da zakarun gaba. Wadannan matasa sun nuna cewa saka jari a ingantaccen ilimi yana haifar da ɗa mai ido.”
Ya kuma bayyana cewa tallafa wa ɗaliban don halartar gasar ta duniya wani muhimmin zuba jari ne ga makomar Jihar Katsina.
Dikko Raɗɗa ya kuma yaba wa Malamin ɗaliban, Yazid Ahmed bisa jagorantar daliban zuwa ga wannan nasara, tare da ƙarfafa gwiwar sauran dalibai da su himmatu wajen neman ƙwarewa a fannonin da suka zaɓa.
