(Ci gana daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Sallama dai masu karatu. Muna godiya da bibiyarmu da ku ke yi. Allah Ya amsa addu’o’in mu. Ya sa mun dace da daren Lailatul ƙadar. Barkanmu da Sallah. Allah Ya maimaita.
Binciken mako 24:
A wani bincike na makonni 24, mata 23 sun sha furotin soya mai ɗauke da isoflavones, yayin da wasu suka sha wani furotin daban. Sakamakon ya nuna:
Raguwar tsananin layukan fuska da kashi 7 cikin 100.
Rage duhun fata da kashi 2 cikin 100.
ƙaruwa a danshin fata har kashi 68 cikin 100 a wani ɓangare na fuska.
Wannan bincike shi ne mafi ƙarfi wajen nuna tasirin isoflavones kai tsaye.
