
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da filin jiragen sama, wato ‘Gateway Cargo International Airport’, wanda Gwamnatin Gwamnan Ogun Dapo Abiodun ta gina a jihar.
Haka kuma Shugaban ya ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu mallakar kamfanin Gateway Airline.
Ya ce: “Jarinmu domin al’ummarmu ne. Ababen more rayuwar da muke ginawa suna nuna imaninmu ga ƙasarmu, da kuma cewa tubalin yau na nufin arziƙin gobe. Na gode muku duka bisa fahimtarku.”
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne cikin gagarumin yanayi a Ƙaramar Hukumar Iperu, inda manyan jami’an gwamnati da shugabanni suka halarta.
Daga cikin su akwai Gwamna Dapo Abiodun, wanda ya bayyana cewa waɗannan ayyuka za su taimaka matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da inganta rayuwar al’umma.
Sabon filin jirgin saman da aka buɗe ana sa ran zai ƙara sauƙaƙa zirga-zirga, janyo zuba jari, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a jihar.
Sannan sauran ayyukan da aka ƙaddamar suna daga cikin shirye-shiryen gwamnati na ƙarfafa ababen more rayuwa da cigaba mai ɗorewa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
