Fursuna ta haihu a kurkuku bayan zargin jami’i da yi mata fyaɗe

Spread the love

An samu wata sabuwar taƙaddama a Jihar Yobe bayan wata fursuna mai suna Blessing Sunday ta haifi ɗa namiji a asibiti, lamarin da ya biyo bayan zargin cewa wani jami’in gidan yari ne ya yi mata fyaɗe har ta samu juna biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa fursunar ta haihu ne a Asibitin Kwararru na Potiskum a ranar Lahadi, inda ita da jaririn ke cikin ƙoshin lafiya. Wata majiya ta tabbatar da cewa an kai ta asibiti cikin lokaci kuma komai ya tafi daidai yayin haihuwar.

Ana zargin cewa lamarin ya samo asali ne tun watan Nuwamban shekarar da ta gabata, lokacin da wani jami’in gidan yari, Sani Saleh-Bodejo, wanda ke aiki a matsayin mai kula da yankin fursunoni, ya shiga ɓangaren mata da daddare tare da aikata lalata da Blessing Sunday. Haka kuma, wasu majiyoyi sun ce an yi hakan ne da taimakon wasu ma’aikata mata a cibiyar.

Baya ga wannan, ana kuma zargin jami’in da yin irin wannan aika-aika da wata fursuna mai suna Salma, abin da ya ƙara dagula lamarin tare da jawo hankalin jama’a.

Bayan bayyanar waɗannan zarge-zarge, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa ta tabbatar da faruwar lamarin tare da ɗaukar matakin dakatar da jami’in da wasu da ake zargi suna da hannu a cikin lamarin. Hukumar ta ce an ɗauki matakin ne bayan nazarin rahoton binciken farko.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar, an jaddada cewa suna da manufar rashin juriya ga duk wani nau’in rashin ɗa’a ko take haƙƙin fursunoni. Hukumar ta kuma tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Lamarin ya sake tayar da tambayoyi a tsakanin jama’a kan tsaron fursunoni, musamman mata, a gidajen gyaran hali, inda wasu ke kira ga ƙarin matakan tsaro da tsauraran hukunci ga masu aikata irin waɗannan laifuka.

By ukarofi