Mutane huɗu sun rasu yayin da ‘yan bindiga suka farmaki ƙauyukan Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mutane huɗu ne suka rasu a wani hari da aka kai a wasu ƙauyuka sa ke Gundumar Gebbe a Ƙaramar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun fito ne daga maɓoyarsu da ke dajin Wawa a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, wadda ke da iyaka da ƙauyukan da lamarin ya shafa a Shanga.

Haka kuma, a yayin harin ne aka ƙone wasu gine-gine da ke ƙauyukan Kalkami, Tungar Bori da Kawara da sauransu.

Bayanai sun tabbatar da cewa ƙari akan Kalkami, maharan sun kuma ƙone ƙauyen Kawara a ranar Litinin.

Sannan, ba a iya ƙididdige adadin waɗanda suka rasu ba a ƙauyukan zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.

Mataimakin Shugaban ƙaramar hukumar Shanga, Adamu Hamza Gebbe ya tabbatar da al’amarin, inda ya ce wannan ba shi en karo na farko ba da ‘yan bindiga ke kai wa yankin hari.

A halin yanzu wasu daga cikin mazauna yankin na gudun hijira a tsibirin Gungu, yayin da wasu ke fakewa a dazuka don aun tsaro, kamar yadda Dagacin Gebbe, Alhaji Haruna Usman ya bayyana wa manema labarai, yana mai tir da faruwar al’amarin.

By Babaji