
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matatar Mai ta Ɗangote ta ɗaga farashin fetur da Naira 75, inda kowace lita ta kai N1,275, yayin da na dizal kuma ya ƙaru da Naira 200, wato ya kai N1,950.
Wani jami’i a matatar ya shaida wa manema labarai a daren Talata cewa wannan ƙara farashi ya samo asali ne daga canjin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da yanayin kasuwa a cikin gida.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da masu amfani ke fuskantar tashin farashin kayan masarufi, inda wannan ƙara zai iya ƙara wa farashin sufuri da sauran kayayyaki nauyi.
A cewar The Punch, jami’in ya tabbatar da cewa ƙarin ya samo asali ne daga sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma yanayin kasuwa.
Wannan ƙarin zai iya haifar da ƙarin hauhawar farashin sufuri da kayan masarufi acikin al’ummar Nijeriya da kewayenta.
