Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, a yau Laraba, ta gudanar da zamanta na Majalisar Dokoki mai lamba 160 a zauren Majalisar Dokoki, wanda hakan ya nuna wani muhimmin mataki na ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a harkokin gudanar da ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
A lokacin zaman, kwamitin majalisar kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu ya gabatar da rahotonsa ta hannun mataimakin shugaban majalisar, Hon. Adamu Aliyu Gummi wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin. Rahoton ya mayar da hankali ne kan binciken da ake yi kan ayyukan kuɗi na ƙananan hukumomi 14 na shekarar kuɗi ta 2025.
Kwamitin ya ba da shawarar dakatar da Shugabannin ƙananan hukumomi guda biyu Hon. Mannir Mu’azu Haidara na ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda da Hon. Umar A. Faru na ƙaramar hukumar Bukkuyum saboda ƙin amincewa da gayyatar da kwamitin ya yi musu da gangan.
An bayar da gayyatar ne domin su ba da bayanai game da kashe kuɗaɗen da aka ware wa Kananan hukumomin su.
Bayan tattaunawa da shugaban majalisar ya jagoranta, Majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin baki ɗaya tare da amincewa da dakatar da shugabannin biyu nan take har sai an kammala binciken.
An umarci jami’an da abin ya shafa da su miƙa ragamar gudanar da ƙananan hukumomin su ga mataimakan hugabannin su ba tare da ɓata lokaci ba.
Majalisar ta gano ayyukan rashin girmamawa ga majalisar dokoki, da kuma rashin gaskiya da riƙon amana, a matsayin manyan laifukan da suka cancanci ɗaukar matakin ladabtarwa.
Bugu da ƙari, majalisar ta yi tattaunawa sosai kan rahoton mai taken “Bincike kan ayyukan kuɗi na kansilolin ƙananan hukumomi 14 na shekara ta 2025” kuma ta yanke shawarar ɗaukar dukkan shawarwarin da ke ciki.
An miƙa ƙudurorin ga hukumar zartarwa don aiwatarwa domin amfanin shugabanci nagari da kuma tsarin kuɗi.
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta sake nanata alƙawarinta na tabbatar da riƙon amana, tabbatar da kula da albarkatun jama’a cikin tsanaki, da kuma kare amanar da jama’a ke bai wa masu riƙe da muƙamai.
