
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke wa wasu mayaƙan Boko Haram guda huɗu hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan sun amsa laifukan da Gwamnatin Tarayya ta tuhumce su a kansu.
Rahotanni sun bayyana cewa, an samu wani shaida daga Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, da ya bayar da hujja yayin gabatar da shari’ar ta ranar Laraba.
Alƙali Omotosho ya kuma yanke wa wasu da ake zargi su 14 hukuncin ɗaurin shekaru 20 zuwa 25 a gidan yari bisa laifuka daban-daban da aka gabatar akansu.
‘Yan ta’addar da aka yanke wa ɗaurin rai-da-ran sune Ali Abiso, Bakura Kabiru, Ado (da aka sani da Luka Garba), da kuma Babagoni Masawai.
Daga cikin laifukan da aka samu Ali Abiso da hannu acikinsu akwai hare-haren da Boko Haram ta ƙaddamar a Bama, Gwoza, Konduga, Bita, Baza, da Aulari a ko kafin ranar 8 ga watan Yulin 2022, waɗanda sun ci karo da sashe na 17 na Haramcin Laifukan Ta’addanci a kundin 2022. Haka ma takwarorin nasa akan makaman laifukan.
Sauran mutane 14 da aka yanke wa hukuncin zaman kurkukun sun haɗa da Ali Mustapha, Danbawa Salisu, Modu Ali, Sanda Bello, Mustapha Fali, Modu Musa, Bidal Modu, Mohammed Abdullahi, Umar Garba, Usman Ahmadu, Hussaini Bukar, Baba Manye, Musa Mai Modu da kuma Ali Musa.
Wannan mataki ya nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke aiki tuƙuru wajen ganin ta gurfanar tare da ɗaukar matakin doka akan waɗanda aka samu da hannu a laifukan da suka shafi ta’addanci a Nijeriya.
