
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta umarci ma’aikatan gwamnati da iyalansu da su fice daga ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja, tana mai kokawa da ƙamarin rashin tsaro a sassan Nijeriya.
A ranar Laraba ma’aikatar ta fitar fa sabon gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘ya’yan Amurka da su kiyaye, yayin da aikata manyan laifuka suka tsananta a sassan Nijeriya waɗanda suka haɗa da ta’addanci, garkuwa, rikicin addini da ƙabilanci da kuma rashin daidaiton al’amura a fannin lafiya a ƙasar.
Akan haka ne ta kirayi Amurkawan da su ƙaurace wa zuwa jihohi guda 23 inda ta kira gargaɗin da “Do Not Travel” zango na uku. Jihohin ta ƙara sun haɗa da Filato, Jigawa, Kwara, Neja da kuma Taraba.
Jihohin ta saka a zango na huɗu sune Borno, Jigawa, Kogi, Kwara, Neja, Filato, Taraba, Yobe, da wasu sassan Adamawa, saboda ta’addanci, fashi da kuma garkuwa da mutane.
A Kudu da Kudu maso Gabas kuwa, akwai Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Inugu, Imo, da kuma Ribas— banda Fatakwal, saboda ayyukan tashin-tashina, garkuwa da dai sauransu.
Haka kuma, ma’aikatar ta yi gargaɗin akwai yiwuwar aukuwar hare-haren ‘yan ta’adda a wajen hada-hadar jama’a kamar kasuwani, wuraren sayayya, otal-otal, wuraren ibada da wuraren manyan taruka.
