Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske kan cece-kuce da suka taso bayan amincewar da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na shirin biyan bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya na kusan Naira tiriliyan 3.3 ga kamfanonin samar da wutar lantarki, wato GenCos.
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an tsara wannan shiri ne domin warware matsalolin kuɗi da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki, tare da tabbatar da daidaito da inganta samar da wuta a ƙasa baki ɗaya.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan shiri na cikin babban tsarin gyaran kuɗaɗen ɓangaren wutar lantarki na shugaban ƙasa, wanda ke da nufin farfaɗo da tsarin samar da wuta, tare da tabbatar da cewa an biya bashin da aka tantance bisa hujja da kwangila.
An riga an fara aiwatar da shirin, inda aka riga aka biya naira biliyan 223, yayin da wasu naira biliyan 197 ke kan hanyar biyan su, musamman waɗanda suka shafi iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da wuta.
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa tun daga shekarar 2015 zuwa 2025, ɓangaren wutar lantarki ya tara bashin kusan naira tiriliyan 4.7. Sai dai bayan wani cikakken bincike da tantancewa da aka gudanar bisa umarnin shugaban ƙasa, an rage wannan adadi da kashi 30 cikin 100, wanda ya kai ga amincewa da biyan naira tiriliyan 3.3 kacal — wato bashin da aka tabbatar da sahihancinsa.
An kuma bayyana cewa biyan bashin ba zai kasance lokaci guda ba, sai dai za a riƙa yi a hankali ta hanyar tsarin kasuwa domin kaucewa matsin lamba ga tattalin arziki.
Ya zuwa ranar 31 ga Maris, 2026, kamfanoni 17 da ke kula da samar da wutar lantarki sun riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar bashin, wanda ya kai kimanin Naira tiriliyan 2.28, abin da ke nuna yadda ake samun haɗin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki a ɓangaren.
Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa wannan shiri ba lada ba ne ga kamfanonin, illa dai wani tsari ne na gyara da sake farfaɗo da ɓangaren wutar lantarki, domin tabbatar da cewa ana biyan kuɗaɗen ne bisa aikin da aka tabbatar an yi.
A gefe guda, shirin yana tafiya tare da wasu sauye-sauye da suka haɗa da gyaran farashin lantarki bisa matakin sabis, tare da samar da tallafi ga talakawa domin rage musu nauyi.
Sai dai duk da wannan bayani, Shugabar ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya, Joy Ogaji, ta nuna damuwa kan yadda aka kai ga ƙididdigar bashin na Naira tiriliyan 3.3, tana mai cewa ba a haɗa su yadda ya kamata a cikin lissafin ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta sanar da wani tsarin biyan bashin ɓangaren wutar lantarki ta hanyar lamunin naira biliyan 501, wanda shi ma ya janyo muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki.
A ƙarshe, Fadar Shugaban ƙasa ta jaddada cewa wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin gina ingantaccen tsarin wutar lantarki mai ɗorewa, wanda zai amfanar da ‘yan Nijeriya gaba ɗaya, tare da dawo da amincewa a ɓangaren.
