Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Laraba ya karɓi bakuncin mambobin jam’iyyar APC da ke Majalisar Wakilai daga jihar, a wani mataki da ake ganin yana da alaƙa da sauye-sauyen siyasa da ke gudana a halin yanzu.
Rahotanni sun bayyana cewa taron ya gudana ne a gidan gwamnan da ke Abuja, a daidai lokacin da ake ƙara jin rade-radin cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.
Da yake magana da ‘yan jarida bayan taron, Dabo Ismail, ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Toro, ya bayyana cewa gwamnan ne ya gayyace su domin tattauna batun sauye-sauyen siyasa da ke gudana, musamman a jihar Bauchi, tare da duba muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban jihar.
Ya ce: “Mun zo ne bisa gayyata ta musamman domin tattauna yadda siyasa ke sauyawa a Najeriya, musamman a Bauchi, da kuma yadda za a magance wasu muhimman matsaloli. Mun cimma wasu matsaya masu kyau.”
Ya ƙara da cewa: “Da yardar Allah, nan ba da jimawa ba za mu bayyana matsayarmu. A halin yanzu za mu ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki, tare da sanar da su sakamakon wannan ganawa.”
Wannan sabon ci gaba ya biyo bayan wasu muhimman ganawa da gwamnan ya yi a kwanakin baya. A ranar 1 ga Afrilu, ya karɓi shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, tare da gwamnan Kano, Abba Yusuf, a gidan gwamnati da ke Bauchi.
Haka kuma, a wani taro da ya yi da mambobin jam’iyyar ADC, gwamnan ya bayyana cewa ya taɓa tunanin komawa APC tare da magoya bayansa, sai dai ya nuna cewa jam’iyyar ba ta buɗe ƙofa sosai gare shi ba, inda ya ce ADC ita ce mafi dacewa a gare shi da mabiyansa.
A gefe guda kuma, wasu jiga-jigan APC a Bauchi sun buƙaci shugabannin jam’iyyar na ƙasa su haɗa su cikin tattaunawar da ake yi kafin ɗaukar duk wani mataki dangane da yiwuwar karɓar gwamnan cikin jam’iyyar.
Wannan jerin ganawa da tuntuba na nuna yadda siyasar Bauchi ke ƙara zafi, yayin da ake shirin babban zaɓen 2027.
