Rikicin ADC: Bangaren Nafiu Bala ya yi zanga-zangar neman INEC ta amince da shi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rikicin shugabanci da yake addabar jam’iyyar adawa ta ADC ya ƙara ɗaukar sabon salo a ranar Alhamis, yayin da wani ɓangare ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya gudanar da zanga-zanga a hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ke Abuja, inda suka nemi a amince da shugabancinsa a hukumance.

Rahotanni sun nuna cewa Nafiu Gombe, tare da haɗin gwiwar ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Kogi, Leke Abejide, da ɗaruruwan magoya baya, sun zargi ɓangaren da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark ke jagoranta da yunƙurin ƙwace ikon jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba, tare da karya kundin tsarin mulkinta da dokokin tafiyarta.

Yayin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, Nafiu Gombe ya buƙaci INEC da ta tsaya tsayin daka wajen bin doka da oda a warware rikicin, yana mai cewa ba za a bari wasu su shigo ta “baya” su karɓe ikon jam’iyyar ba.

Ya ce, “Mun zo ne domin mu roƙi INEC ta bi doka da ƙa’ida. Ba za a zo a karɓe jam’iyya ta hanyar da ba ta dace ba ba. Mu ’yan dimokuraɗiyya ne, ba ma son masu kuɗi su lalata tsarin dimokuraɗiyya. ADC ta kowa ce—tun daga matakin mazaɓu har zuwa na ƙasa.”

Shi ma a nasa jawabin, Leke Abejide ya buƙaci hukumar zaɓen da ta kare dimokuraɗiyya daga hannun waɗanda ya kira ‘masu ƙwace iko’, yana mai jaddada cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya fayyace ƙa’idojin cancantar riƙe muƙamai.

Ya ce, ba zai yiwu mutum ya shigo jam’iyya da rana tsaka ya nemi jagoranci ba, yana mai ƙara da cewa dole ne mutum ya yi aƙalla shekaru biyu a matsayin cikakken ɗan jam’iyya kafin ya nemi kowane muƙami.

A wani ɓangare kuma, Daraktan Matasa da Wayar da Kai na jam’iyyar ADC, Mohammed Sahad, ya yaba wa INEC kan bin umarnin kotu, amma ya nemi ta ƙara da amincewa da Nafiu Bala Gombe a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Sai dai da yake mayar da martani a madadin INEC, Kwamishinan Hukumar na ƙasa, Abdullahi Abdu Zuru, ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa hukumar za ta duba buƙatunsu tare da ba su amsa cikin lokaci.

Wannan zanga-zanga na zuwa ne kwana guda bayan wani ɓangaren jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark ya gudanar da irin tasa zanga-zanga a Abuja ƙarƙashin taken #OccupyINEC, inda suka zargi hukumar da katsalandan cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar.

Lamarin na nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara tsananta a ADC, abin da ke barazana ga haɗin kan jam’iyyar gabanin zaɓuɓɓuka masu zuwa.

By ukarofi