Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Nijeriya ce ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen ɓarnar abinci, inda ake asarar kusan tan miliyan 38 na abinci a duk shekara, kamar yadda ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bayyana.
An bayyana wannan adadi mai tayar da hankali ne yayin bikin ranar Ranar Rage Shara ta Duniya (International Zero Waste Day) da aka gudanar a birnin Abuja, inda masu ruwa da tsaki suka yi kira da a ɗauki matakai cikin gaggawa da haɗin gwiwa domin rage ɓarnar abinci da kuma inganta yadda ake amfani da albarkatu yadda ya kamata.
Taron, mai taken rage ɓarnar abinci da amfani da shi yadda ya dace, ya haɗa wakilai daga Gwamnatin Tarayya, Hukumar Bunƙasa Masana’antu ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNIDO), da sauran abokan hulɗa na ci gaba, domin tattauna girman matsalar da kuma hanyoyin magance ta.
Mataimakin jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, Zissimos ɓergos, ya bayyana cewa yawan ɓarnar abinci a Nijeriya abin damuwa ne ƙwarai. Ya ce ba wai asarar abinci kaɗai ake yi ba, har ma ana ɓata albarkatu masu muhimmanci kamar ruwa, makamashi, ƙwadago da jari.
Ya ƙara da cewa, a duniya baki ɗaya, a shekarar 2022 kaɗai, kusan tan biliyan ɗaya na abinci – wato kusan kashi ɗaya cikin biyar na duk abincin da ake samarwa – ya lalace ko aka jefar.
A cewarsa, wannan ba kawai ɓarnar abinci ba ce, illa ce ga ƙoƙarin yaƙi da yunwa, tare da barazana ga lafiyar muhalli. Ya kuma gargaɗi cewa ɓarnar abinci na taka rawa sosai wajen gurɓata muhalli, inda take haifar da kusan kashi 10 cikin 100 na hayaƙin ɗumamar yanayi a duniya, wanda ya fi sau biyar na jiragen sama, kuma kusan kashi 40 cikin 100 na hayaƙin methane.
Ya ce, irin waɗannan hayaƙai na ƙara ta’azzara sauyin yanayi tare da kawo cikas ga ƙoƙarin gina tattalin arziki mai ɗorewa ba tare da shara ba.
Duk da haka, ɓergos ya yaba da matakan da Nijeriya ta fara ɗauka, ciki har da shirin tattalin arzikin sake sarrafa kaya (Circular Economy Roadmap), kafa kwamitin haɗin gwiwar ma’aikatun gwamnati kan wannan tsari, da kuma yunƙurin ƙirƙirar dokar kula da shara ta roba a ƙasa.
A nasa jawabin, Ministan Muhalli na Tarayya, Balarabe Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnati na magance matsalar ɓarnar abinci a matsayin wani ɓangare na gyaran muhalli da tattalin arziki.
Ya ce ɓarnar abinci na da illa ga muhalli da tattalin arziki da zamantakewar al’umma, yana mai cewa duk abincin da aka jefar na nufin an ɓata albarkatu, alhali kuwa har yanzu ’yan Nijeriya da dama na fama da ƙarancin abinci.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta fara aiwatar da wasu shirye-shirye na rage ɓarnar abinci a manyan kasuwanni a faɗin ƙasar, musamman wajen rage asarar amfanin gona bayan girbi.
Shi ma Daraktan ofishin UNIDO na yankin Nijeriya, Philbert Johnson, ya jaddada muhimmancin tsarin abinci mai inganci, yana mai cewa abinci ba kawai kayan ci ba ne, ginshiƙi ne na arziki, lafiya da tsaro.
Ya ƙara da cewa, idan tsarin samar da abinci ya lalace, tasirinsa na shafar tattalin arziki, muhalli da rayuwar al’umma baki ɗaya.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa UNIDO za ta ci gaba da tallafa wa Nijeriya wajen gina tsarin noma da masana’antu mai ɗorewa, wanda zai anfani kowa da kowa.
