Da Ɗumi-Ɗumi: Kanal na soja da wasu dakarun tsaro sun rasu a sabon harin Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mayaƙan Boko Haram sun halaka Kanal I.A. Muhammad na Rundunar Sojin Nijeriya da wasu sojoji da dama a yayin wani hari da suka kai cikin dare a wani sansanin sojoji da ke Monguno a Jihar Borno.

A daren ranar Lahadi wayewar Litinin ne maharan suka kai farmakin akan Forward Operating Bas (FOB) da ke ƙarƙashin Bataliya ta 242 a Mungunu, wanda ya sauka akan sashe na 3 na ayyukan atisayen sojoji yayin aikin daƙile ta’addanci.

Wasu sojoji da aka tura fage fama a yankin Arewa ta Gabas sun bayyana wa ShaharaReporters a yau Litinin yadda aka halaka babban sojan yayin da yake jagorantar atisayen daƙile harin ‘yan ta’adda.

Majiyoyi sun bayyana cewa, a yayin harin, maharan sun nufi wata ƙaramar tawaga ce, lamarin da ya tilasta yin kiran gaggawa domin ƙarfafa adadin jami’an da ke yankin.

A yayin da tawagar kanal ɗin ta tunkari wajen ne sai ta taka wani waje da mayaƙan suka dasa ababen fashewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun tsaro da dama ciki har da jagoran nasu.

Wannan hari ya nun yadda mayaƙan ‘yan ta’adda ke cigaba da amfani da boma-bomai wajen aiwatar da ayyukansu, wanda ke nuna rashin tsaro ga kariyar dakarun da ke tsaron shiyyar.

By Babaji