‘Tun da jimawa mutane suka bar ƙauyen’: Sojoji sun yi ƙarin haske kan harin da shaidu suka ce ya halaka sama da mutane 56

Spread the love

Rundunar sojin Nijeriya ta kare harin jirgin sama da aka kai kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe, inda aka ce mutane da dama sun rasu tare da jikkata.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa harin ya gudana ne yayin wani farmakin da aka kaddamar kan wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a yankin.

Sai dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin, tana zargin cewa sama da mutane 100 ne suka mutu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Sani Uba, ya fitar, ya ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan leken asiri da suka nuna cewa yankin Jilli ya zama mafaka da cibiyar hada kayan aiki na ‘yan kungiyar ISWAP.

Sojojin sun ce wurin ya dade yana zama hanyar zirga-zirga da haduwar ‘yan ta’adda, musamman bayan hare-haren baya-bayan nan da suka hada da na’urorin fashewa da kuma farmaki a Ngamdu da Benisheik.

Sun ƙara da cewa, an gudanar da harin cikin tsanaki tare da tabbatar da ingancin wurin da aka nufa, inda suka ce an hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata motocinsu, yayin da sauran suka tsere.

Har ila yau, rundunar ta ce an kama wani da ake zargi mai suna Turja Bulu, wanda ake zargin yana taimaka wa ‘yan ta’adda wajen jigilar kayan aiki, kuma ya amsa laifinsa a wani hari da ya gabata.

Sojojin sun jaddada haramcin amfani da babura a yankin arewa maso gabas, musamman a jihohin Borno da Yobe, saboda alakar su da ayyukan ‘yan ta’adda, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

By Babaji