Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da kwamitin aikin hajji na 2026 ƙarƙashin shugabancin tsohon kwamishinan Shari’a, Barista Ahmed Usman El-Marzuq.
‘Yan kwamitin sun haɗa da Ali Isah,Amadu Ahmed Diddiri, Ali Sani Ahmed, Hajara Hajjo Lawal da Murna Ibrahim Duwan.
Sauran sun haɗa da Mairo Ibrahim,Abduljalal Haruna Runka, Ahmed Tijjani Abdulkadir, Yusuf Ibrahim Safana Sai Abubakar Yusuf da zai zama sakataren kwamitin.
A jawabinsa a wajen taron Gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci ‘yan kwamitin da su tabbatar da zirga zirga da kula da jin daɗin maniyata ba tare da an sami matsala ba.
Ya kuma umurci ‘yan kwamitin da su kasance masu kula da taimakawa wajen hidimar maniyata a ƙasa mai tsarki har lokacin da za su dawo Nijeriya.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin kuma Amirul Hajji Barista Ahmed Usman El-Marzuq yayi godiya ga Gwamna Dikko Raɗɗa bisa wannan matsayi da ya basu,ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa shi da yan kwamitin za su yi iyakar ƙoƙarin su domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin hajji na bana.
Bikin ya sami halartar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt Hon Nasiru Yahaya,kwamishinonin da sauran manyan jami’an gwamnati.
