Gwamnatin Kaduna ta shirya taron wayar da kai kan alaƙar amfani da muggan ƙwayoyi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Hana Sha da Kula da matsalolin tabuwan hankali na jihar Kaduna KADSAMHSA ta bayyana cewa ta shirya taro domin wayar da kan mutane domin samar wa mata kariya daga kamuwa da cututtuka kamar su Kanjamau da hepatitis.

Shugaban Hukumar Joseph Ike ya sanar da haka a ranar farko na taron tattauna alakar amfani da muggan kwayoyi da kamuwa da cututtuka .

Ike ya ce matan dake amfani da muggan kwayoyi na daga cikin rukunin mutanen dake da wahalar samu musamman a Arewacin Nijeriya.

Ya ce alkalumar binciken da Cibiyar UNODC da ma’aikatar lafiya ta Gwamnatin Tarayya suka fitar a shekarar 2020 ya nuna cewa a cikin mutum hudu masu amfani da muggan ƙwayoyi akwai mace daya.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ta rawaito cewa taron wanda aka shirya tare da hadin gwiwar kungiyar Lafiya ta SFH ya samu halartan masu ruwa da tsaki daga jihohin Gombe, Abia, Oyo da Kaduna.

An shirya taron ne domin hada kan gwamnatocin domin ganin an tattauna hanyoyin da suka fi dacewa wajen shawo kan matsalar.

“Taron zai bukaci kwarewar masu ruwa da tsaki domin gano matakan da suka fi dacewa wajen dakile yaduwar cututtukan Kanjamau da Hepatitis ta hanyar inganta bada magungunan cututtukan, inganta shirye-shiryen wayar da kan mutane domin guje wa amfani da allurar da sauran su.

“Burin taron shine rage aukuwar matsalolin da mata masu ta’amali da muggan kwayoyi ka iya samu da tsaro hanyoyin da za a samar da kudaden da za a bukata domin ganin shirin ya yi aiki yadda ya kamata.

Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar Hajiya Umma Kaltum-Ahmed ta ce biyan bukatun matan dake amfani da muggan kwayoyi haƙƙi ne da ya kamata da inganta lafiya.

Kaltum ta ce gudanar da wannan taro na da mahimmanci musamman a wannan lokaci da Nijeriya ke fama da matsalolin raguwa a tallafin da take samu daga kasashen waje.

Ta ce wannan shiri zai dawama ne idan har an mike tsaye wajen ware kudade da hadin hannun kowace fannin.

By ukarofi