* Ta yaba wa gwamnati kan shirye-shiryen lafiya da ilimi
Daga RABIU SANUSI a Kano
Daraktan Hukumar ƙididdiga ta Jihar Kano, Dr. Surajo Sulaiman, ya sake jaddada ƙudirin hukumar na ƙara zage damtse wajen wayar da kan al’umma, bunƙasa haɗin kan jama’a, da kuma tallafawa manyan shirye-shiryen ci gaban gwamnati a faɗin jihar.
Da yake bayani kan ayyukan hukumar, Dr. Sulaiman ya bukaci al’ummar jihar da su hada kai wajen magance matsalolin da ke addabar yankunansu, yana mai cewa cigaba mai dorewa ba zai samu ba sai da hadin kai da jajircewar jama’a.
Ya shawarci al’umma da su rika kafa kwamitoci a matakin unguwanni domin isar da koke-kokensu, buƙatunsu da shawarwarinsu ga hukumomin da suka dace. Ya jaddada cewa tsari mai kyau na sadarwa na taka muhimmiyar rawa wajen samun saukin matsaloli da cimma ci gaba.
A cewarsa, hukumar na amfani da hanyoyi daban-daban wajen wayar da kan jama’a kan muhimman batutuwa, musamman a fannoni na lafiya, tsaftar muhalli da walwalar al’umma.
Sai dai ya amince cewa akwai kalubale da hukumar ke fuskanta, musamman wajen kara wayar da kan jama’a domin su dauki nauyin kula da lafiyarsu da tsaftace muhallansu.
Dr. Sulaiman ya kuma bayyana cewa a kokarin da gwamnati ke yi na yaki da cutar zazzabin cizon sauro, musamman domin kare lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara, an kafa wani kwamiti karkashin hukumar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi domin tattara bayanai da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar a faɗin jihar.
Ya ce bayanan da za a tattara za su taimaka wa gwamnati wajen daukar matakan da suka dace, ciki har da rabon magunguna kyauta, gidajen sauro, da kuma feshi da maganin sauro a sassa daban-daban na jihar.
Daraktan ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarin da yake yi wajen sauke nauyin ‘yan fansho a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Haka zalika, ya jinjinawa gwamnan kan daukar nauyin karatun dalibai zuwa kasashen waje, da kuma biyan kudin jarabawar WAEC da NECO ga daliban jihar.
A ƙarshe, Dr. Sulaiman ya yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai, tare da bayar da shawarwari masu anfani da goyon baya, domin samun zaman lafiya, cigaba da wadata a jihar.
