An maka mataimakin gwamnan Zamfara ƙara bisa zargin ɓata sunan tsohon ɗan majalisa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Yusuf Alasan Kanoma, ya shigar da ƙarar mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai da sadarwa ga Gwamnan Jihar Zamfara, Mustafa Jafaru Kaura a gaban Kotun Majistare ta ɗaya da ke Gusau, kan zargin barazana ga rayuwarsa da kuma ɓata masa suna.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a yau Talata a Kotun Majistare ta ɗaya, jim kaɗan bayan fara sauraron shari’ar da ke gaban kotu, lauyan mai ƙara, Barista Surajo Garba Gusau, ya bayyana kalaman da Mustafa Jafaru Kaura ya yi wa Hon. Alasan a shafukan sada zumunta a matsayin laifi mafi hatsari da yunkurin ɓata sunan mutum.

Barista Gusau ya ƙara da cewa, a zaman farko, wanda ake ƙara ya gaza bayyana a gaban kotu kuma bai aika da wakilcin lauyansa ba.

“Lokacin da muka tambayi kotu ko an baiwa wanda ake ƙara takardar sammace, kotu ta gano cewa duk wani ƙoƙari na neman kai sammacen gareshi yaci tura”. Ya ce

Ya bayyana cewa kotun, bayan neman izinin ta, ta ba da umarnin a maye gurbin sammacin ta hanyar liƙa sammacin a kofar gidan wanda ake tuhuma watau Mustafa Jafaru Kaura.

“Fata na shine a yi adalci a kan lamarin”. Ya ƙara da cewa

Barista Gusau ya ƙara da cewa alƙalin kotun Mai Shari’a Murtala Abdullahi ya ɗage shari’ar zuwa ranar 27 ga wannan watan don ci gaba da sauraron ƙarar.

By ukarofi