Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa rawar da mata ke takawa da kuma haɗa su cikin harkokin siyasa da shugabanci a faɗin jihar.
Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na gidan gwamnatin Katsina ya haɗa da manyan masu ruwa da tsaki na mata, shugabannin jam’iyyun siyasa da jami’an gwamnati da mata ƙarƙashin ƙungiyar Reserved Seats for Women Association wanda uwargidan Gwamnan jihar Hajiya zulaihatu Dikko Raɗɗa ta jagoranta.
Tattaunawa a wajen taron yafi mayar da hankali ne kan faɗaɗa rawar mata a shugabanci, shiga siyasa da kuma yanke shawara a cikin harkokin gwamnati a jihar.
Haka kuma, taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnati ke ci gaba da yi domin inganta shugabanci mai haɗin kai da ƙara samar da dama ga mata a cikin tsarin dokokin zaɓe na jam’iyyun siyasa.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa haɗa mata cikin siyasa wani ginshiƙi ne na bunƙasar dimokuraɗiyya da ingantaccen shugabanci, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da damar da ta dace ga kowa.
Ya kuma lura cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samar da dama mai kyau ga mata domin shiga da kuma tsayawa takara ba tare da wariya ba.
“Babbar jam’iyyarmu ta samar da dama da izini ga mata su fito su nemi muƙamai cikin ‘yanci. Wannan wata alama ce ta ƙudirinmu na haɗin kai da daidaito a harkokin siyasa,” in ji gwamnan.
Ya bayyana cewa tsarin zaɓen ‘yan takara yana gudana ne bisa tanade-tanaden dokar zaɓe, wadda ya amince da hanyoyi guda biyu kacal—zaɓen fidda gwani (primary elections) ko kuma tsarin sulhu (consensus).
“Kamar yadda dokar zaɓe ta tanada, hanyoyi guda biyu ne kawai ake amfani da su wajen zaɓen ‘yan takara—ko dai ta zaɓen fidda gwani ko kuma ta hanyar sulhu,” ya ƙara da cewa.
Gwamna Raɗɗa ya amince da cewa akwai ƙalubale da ke hana mata cikakken shiga siyasa, yana mai cewa waɗannan matsaloli na buƙatar ci gaba da tattaunawa da haɗin kai domin shawo kansu.
Ya kuma nuna damuwa cewa a wasu lokuta, muƙaman da aka ƙirƙira domin ƙarfafa mata ba lallai ne mata ne ke rike su ba.
“Abin takaici ne cewa a wasu lokuta, muƙaman da aka tanada domin inganta muradun mata ba su hannun mata suke ba,” in ji shi.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin ƙuri’un mata, yana mai cewa mata su ne mafi rinjaye a yawancin rumfunan zaɓe a faɗin jihar.
Ya kuma yaba da halayen mata a shugabanci, ciki har da ladabi, jajircewa da kuma iya yanke hukunci cikin daidaito.
“Daga gogewata a shugabanci, mata masu jajircewa ne, masu aminci kuma suna kawo daidaito wanda yake da matuƙar muhimmanci ga ingantaccen shugabanci,” Dikko ya ce .
Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa shugabanci yana nuni da muradin jama’a, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin shawarwari da jama’a domin cimma abin da suka fi so.
“Ba ni da ikon tilasta wa kowa ya goyi bayan wani ɗan takara. Abin da zan iya yi shi ne yin shawarwari domin fahimtar abin da jama’a suke so,” in ji shi.
Ya ƙarfafa wa mata gwiwa su mai da hankali, su ƙara kwarewarsu, tare da shiga siyasa sosai.
Gwamnan ya kuma yi kira da a yi haƙuri da haɗin kai yayin da harkokin siyasa ke ci gaba, yana mai fatan samun sakamako mai haɗin kai.
“Tare, za mu tabbatar da tsarin siyasa mai gaskiya, mai haɗin kai da nasara domin amfanin jiharmu,” in ji shi.
