Ta’addanci: Remi Tinubu ta nemi taimakon limaman coci na duniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ƙasashen duniya da su fahimci matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta yadda ya dace, tare da kauce wa jirkitar da bayanai da ka iya kawo cikas ga samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ta karɓi bakuncin tsohon Archbishop na Canterbury, Rt. Rev. Justin Welby, a Abuja, a wata ganawa da ta mayar da hankali kan tattaunawar addinai da hanyoyin samar da zaman lafiya.

A cewar mai taimaka mata na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Busola Kukoyi, Uwargidan Shugaban ƙasa ta jaddada cewa fahimtar sahihin yanayin matsalolin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen samar da mafita mai inganci.

Ta ce, “Dole duniya ta fahimci ainihin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta domin a samu mafitar da ta dace,” tare da ƙara da cewa sauraron ɓangarori daban-daban na da muhimmanci kafin yanke hukunci kan rikice-rikice.

Ta kuma yaba wa Welby bisa ra’ayinsa na cewa ’yan Nijeriya su ne suka fi dacewa da warware matsalolin ƙasar, tare da jaddada muhimmancin tattaunawa da za ta ƙara haɗa kai.

Uwargidan Shugaban ƙasar ta kuma yaba wa dakarun sojin Nijeriya kan sadaukarwar da suke yi wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da kira ga cibiyoyin addini a duniya da su riƙa yin da’awar da ke ƙarfafa zaman lafiya.

A nasa ɓangaren, Welby ya ce ziyararsa wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta zaman lafiya da kuma ƙarfafa matsayin Nijeriya a matsayin ƙasa mai mutunta ’yancin addini.

Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da wani sabon taron tattaunawar addinai a birnin London ƙarƙashin jagorancin Global Forum for Peace, inda shugabannin addinin Musulunci da Kirista za su tattauna kan hanyoyin magance rikice-rikicen addini a duniya.

A wani ɓangare kuma, Uwargidan Shugaban ƙasa ta karɓi Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani, wanda ya yi mata bayani kan shirin Girls in Tech, tare da shirin shirya wani liyafa domin nuna sabbin kirkire-kirkire da mahalarta shirin suka samar.

By ukarofi