Tinubu ya nemi sahalewar majalisa domin karɓo bashin Dala miliyan 500

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawan ta amince da ciyo bashin fiye da dala miliyan 516 daga babban bankin Jamus (Deutsche bank), domin aikin wani ɓangare na babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagry.

A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Godswil Akpabio, Shugaban ƙasar ya ce an tsara aikin gina kilomita 100 na titin ne domin ya haɗa Arewa maso yammacin ƙasar da Kudu maso Yammaci.

A cewar sa, babbar hanyar za ta taso ne daga Illela a jihar Sakkwato, ta bi ta jihohin Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun, ta kare a Badagry da ke Jihar Legas.

A cewar wasiƙar, za a yi amfani da bashin wajen gina sashe na 1, rukuni na 1 da na biyu, mai nisan kilomita 120, cikin baki ɗaya kilomita 1,000.

Za a biya bashin ne cikin shekaru 9, amma za a iya ƙara lamunin aƙalla shekaru uku.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni Majalisar ministocinsa ta amince da tsarin karɓo bashin, inda ya buƙaci Majalisar Dattawan ta sanya bashin cikin tsarin karbo bashi na ƙasar.

Wasiƙar shugaban ƙasar ta bayyana cewa babbar hanyar za ta taimaka wajen bunƙasa kasuwanci, da samar da isashen abinci, da haɗin kan ƙasa.

Sanata Akpabio ya miƙa buƙatar ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, kuma ana sa ran zai bayar da rahoto nan da mako guda.

By ukarofi